Inyamuran Arewa Sun Karyata Batun Goyon Bayan Tinubu a Zaben 2023

Inyamuran Arewa Sun Karyata Batun Goyon Bayan Tinubu a Zaben 2023

  • Gabannin babban zaben 2023, kungiyar Inyamurai a jihohin arewa 19 da Abuja sun magantu a kan rade-radin cewa suna goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu
  • Kungiyar ta ce har yanzu bata tsayar da wani dan takara da take goyon baya domin zama magajin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba
  • Don haka, ta ce batun lamuncewa dan takarar shugaban kasa na APC kanzon kurege ne mara tushe balle makama

Kungiyar Inyamurai mazauna jihohin arewa 19 da babban birnin tarayya ta karyata batun lamuncewa takarar shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A wata sanarwa daga Cif Chi Nwogu da Austin Ifedinezi Oforkansi, shugaba da sakataren kungiyar, sun bayyana batun goyon bayan Tinubu a matsayin kanzon kurege, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Bola Tinubu
Inyamuran Arewa Sun Karyata Batun Goyon Bayan Tinubu a Zaben 2023 Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Kungiyar ta bayyana cewa wani Mista Collins Ajali ya yi ikirin cewa kungiyoyin Inyamurai a arewa za su yi wa Tinubu aiki don lashe zaben shugban kasa da kuma tazarcen Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ina Da Tabbacin APC Za Ta Lashe Zabe a Jihar Zamfara, Buhari

Wani bangare na jawabin na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu Inyamurai a jihohin arewa 19 da Abuja karkashin inuwar Igbo Delegates Assembly (IDA) muna watsi da matakin wata kungiya karkashin jagorancin Collins Chibueze Ajali wanda suka ce suna wakiltan kungiyoyin."

Ba mu tsayar da dan takara ba har yanzu, kungiyar Inyamurai

Kungiyar ta kara jaddada cewar daukacin kungiyoyin Inyamurai a jihohin arewa 19 wadanda ke karkashin inuwar IDA basu lamuncewa kowani dan takara na zaben shugaban kasa na 2023 ba, rahoton The Guardian.

Ina da yakinin APC za ta lashe zabe a jihar Zamfara, Buhari

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna karfin gwiwar cewa jam'iyyar APC za ta yi nasara a jihar Zamfara a babban zaben 2023 mai zuwa.

Tinubu ya bukaci daukacin al'ummar jihar Zamfara da yan Najeriya da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki domin zai kawo gagarumin sauyi a kasar.

Kara karanta wannan

Muna Rokanka Kaje Ka Huta Karka Yiwa Tinubu Yakin Neman Zabe - PDP Ga Buhari

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da ministan sadarwa, Isah Pantami ya wakilce shi wajen bude ofishin yakin neman zaben shugabancin Tinubu/Shettima a garin Gusau.

A nashi bangaren, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya ce a yanzu APC ce ke da jihar domin jam'iyyun adawa basu da wani katabus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: