Kai Hare-Haren Ofishoshin INEC: Ya Kamata A Binciki Jam'iyyar PDP Ko Kuma Ta Amsa Wasu Tambayoyi

Kai Hare-Haren Ofishoshin INEC: Ya Kamata A Binciki Jam'iyyar PDP Ko Kuma Ta Amsa Wasu Tambayoyi

  • An bukaci da hukumomin tsaro a kasar nan da suyi gaggawar kiran jam'iyyar PDP dan ta amsa wasu tambayoyi
  • Fetus Keyamo mai magana da yawun dan takarar jam'iyar APC na shugaban kasa ne yayi wannan kiran a wata sanarwa da ya fitar
  • A cewarsa dole ne jam'iyyar PDP ta fitar da wanda tasan suna kai hare-hare ofisoshin zabe da kuma lalata kayan zaben

Abuja: Jam'iyyar APC tayi kira ga hukumomin tsaro da suka hada da DSS, 'Yan sanda, da duk hukumomin tsaron kasar nan kan su tuhumi jam'iyyar adawa ta PDP.

Wannan na kunshe cikin wata takarda da jaridar Legit.ng ta samu wanda take dauke da sa hannun Festus Kyamo mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC.

Festus
Yakamata Hukumomin Tsaro Suyi Gaggawar Kiran Jam'iyyar PDP Dan Amsa Wasu Tambayoyi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Tace Batun Gwamnan Babban Banki Yana Gaban Kotu, Dan Haka Ita Nata Sa Ido

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan zaku iya tunawa jaridar Legit.ng ta rawaito yayin da jam'iyar PDP take taro tace jam'iyyar APC ke da alhakin hare-haren da ake kaiwa ofisoshin zabe

Sanarwa da ya fitar tace:

"Daga wata majiya da muka samu sahihiya ta ta nuna yada wasu dai-daiku ke son durkushe yunkurin hukumar zabe wajen gudanar da zabe, wanda ya hada da lalata kayan aikin kona ofisoshin hukumar da dai sauransu, dan haka muke kira da hukumomin tsaro da suyi duk mai yiwuwa wajen ganin sun tuhumi jam;iyyar kan wannan batu."

Keyamo ya ci gaba da cewa bai kamata ace jam'iyyar PDP tana wasa da hankalin mutane kan zaman lafiya ko tsaro ba.

Kamar yanzu da suke sawa ake kai hare-hare da lalata kayan aikin zabe da ma yunkurinsu na hana zaben duk bai kamata ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Adadin Kujerun Da Jam'iyyar APC Za Ta Lashe

Atiku Ya Bayyana Abinda zaiyi in ya fadi zabe

A wani labarin kuma tsohon mataimakin shugaban kasa wanda ya nemi takarar shugaban kasa har sau shida wanda Shugaba buhari ya kayar da dashi.

Atiku yace indai da rai da lafiya zai ci gaba da neman takarar shugaban kasar Nigeria da duk iya karfinsa.

Amma duk da haka an jiyo Atikun na cewa wannan shine karonsa na karshe da zai nemi takarar shugaban kasar Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida