Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam'iyyar APC Yace Shi Bazai Yi Alkawarin Yin Komai Ba

Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam'iyyar APC Yace Shi Bazai Yi Alkawarin Yin Komai Ba

  • Dan takarar gwaman jihar kano a jam'iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yace shi bazai yiwa al'umma jihar Kano alkawari ba.
  • Gawuna yace shi bazai yi yaudara ba, idan ya ci zaben ya kasa, kuma mutane zasu ga kamar ya yaudaresu.
  • Yace shi iya abinda yasan zai iya shi zai fada, kuma zai tsaya akan muraddin sa wanda yasan na daidai ne da kuma aiki da shawarwari.

Abuja: Dan takarar gwamnan jihar kano a jam'iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yace bazai dauki alkawari kan abinda yasan karyane, ko ba dai-dai bane ga al'ummar jihar kano.

Gawuna, na wannan batun ne a wani taron jin abubuwan da ya shirya gabatarwa jama'ar jihar kano indan yaci zabe, da 'yan kano mazauna Abuja suka shirya masa.

Kara karanta wannan

Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023

Yayin da yake amsa wasu tambayoyi a wani fefain bidiyo da da dan jaridar VOA, Nasiru El-Hikaya yayi masa mai tsawon mintuna bitu, gawuna yace:

"Mu bamu da tunanin son kai, iya abinda zamu iya shi zamu fadawa mutane zamuyi."

Dan jaridar ya cigaba da tambayarsa kan batun da yayi na cewa bazai tonawa kansa rami ya fada a binneshi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gawuna
Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam'iyyar APC Yace Shi Bazai Yi Alkawrin Yin Komai Ba Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Dan takarar gwamnan ya amsa tambayar da bayani kaman haka:

"Bazamuyi alkawuran da muka san baza mu cika su ba, ko kuma alkawura na karya kace zaka yiwa mutane kaza, amma kasan karya kake."
"Mutane na ganin muna cikin gwamnati, zasu kawo mana abinda suka san baza mu iya yi ba, amma zasu so ace tunda muna gwamnati muce musu sai mun zama tukunna, za'a yi su"

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai ya Sha Alwashin Barin Jihar Kaduna, Ba Zai Shiga Lamarin Mulki ba Bayan Cikar Wa'adinsa

"To mu baza muyi yaudara ba, mu hakawa kanmu rami muce zamuyi kaza kuma muzo mu kasa, ka mu fada kuma za'a binnemu"

Gawuna ya ci gaba da fadi:

"ka fadawa mutane gaskiya kan abubuwan da kake son yi da kuma aiyukan da zakai musu wanda kansan zaka iya, domin Allah ne ke bayarwa ba zancenka ba."

Kalli bidiyon a kasa:

Kana Ganin zaka kawo Jihar Kano Ko Ta Yaya Duba Da Yadda Kuke Da Gwamnati?

A siyasar Nigeria mutane na ganin duk wanda gwamna mai ci a jiha ya tsayar sune akasari suka fi cin zabe a jihohin, duk da batun ya fara canjawa a wasu daga cikin jihohin Nigeria.

Misali jihar Jigawa da tsohon gwamnanta Sule Lamido ya tsayar da dan takararsa Aminu Ringim a 2015 kuma ya fadi.

Da Nasiru El-hikaya yake tambayar Gawuna kan batun dacewarsa ko cin nasarar sa, Gawunan ya bada amsa kaman haka:

"Tsarkake niyya da kudiri mai kyau, kuma bana tunanin kowa, ni kawai tunani na shine Allah ne mai yi kuma shine wanda kadai zai amince min nayi."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida