Waiwaye: Jerin Sunayen Fitattun 'Yan Siyasan Najeriya 8 da Suka Rasu a 2022

Waiwaye: Jerin Sunayen Fitattun 'Yan Siyasan Najeriya 8 da Suka Rasu a 2022

Yayin da shekarar 2022 ke zuwa karshe, bari mu duba mu yi waiwayen baya kan fitattun 'yan siyasan Najeriya da suka rasa rayukansu a cikin shekarar.

Ganin cewa wadannan 'yan siyasan ba zasu ga zaben 2023 mai zuwa ba ya kasance abinda yasa za mu koma baya mu waiwaye su.

Fiattun 'yan siyasa
Waiwaye: Jerin Sunayen Fitattun 'Yan Najeriya 8 da Suka Rasu a 2022. Hoto daga Demola Seriki, Arthur Nzeribe, Paul Onongu, Ernest Sonekan
Asali: Facebook

Wannan ya biyo bayan gudumawa da kuma karfin da suke da shi a siyasar da kuma wanda zasu iya bayarwa domin ganin sabon shugaban kasar Najeriya ya bayyana.

Ga jerin sunayen fitattun 'yan siyasar Najeriya da suka rasa rayukansu a shekarar 2022:

  1. Tsohon shugaban kasa Ernest Shonekan

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Najeriya ta tafka asarar daya daga cikin tsofaffin shugabannin kasar wanda ya rike gwamnatin rikon kwarya, Cif Ernest Shonekan a ranar talata, 11 ga watan Janairun 2022 yayin da yake da shekaru 85 a duniya.

Kara karanta wannan

Kaduna: ‘Yan Chana da Suka yi Wata 6 Hannun Masu Garkuwa da Mutane Sun Shaki Iskar ‘Yanci

2. Arthur Nzeribe

Fitaccen 'dan siyasa ne kuma 'dan kasuwa. Arthur Nzeribe ya rasu yana da shekaru 83 a ranar 8 ga watan Mayun 2022 a Oguta dake jihar Imo.

Duk da yayi ta kokarin hana zaben 12 ga watan Yunin 1993, lauyan yana da matukar hazaka da gogewa a fannin siyasa.

3. Vincent Ogbulafor

Ogbulafor tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne na kasa wanda ya rasu a ranar 6 ga watan Oktoban 2022 a Canada yayin da yake da shekaru 73 a duniya.

'Dan asalin Olokoro dake karamar hukumar Umuahia ta kudu a jihar Abia, Ogbulafor a yayin rayuwarsa ya sanar da cewa babbar jam'iyyar adawar za ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 40 a jere.

4. Cif Mbazulike Amechi

Amechi tsohon ministan sufurin jiragen sama ne na jamhuriya ta farko kuma dattijon yankin Kudu maso gabashin Najeriya ne wanda ya rasu a ranar 1 ga watan Nuwamban 2022 yana da shekaru 93 a duniya.

Kara karanta wannan

Mulki har sau 2: Jonathan ya aike da wani muhimmin sako mai daukar hankali ga Buhari

Amechi ya taba jagorantar dattawan kasar Ibo wurin rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saki Nnamdi Kanu, shugaban 'yan awaren IPOB.

5. Paul Unongo

Cif Paul Iorpuu Unongo, tsohon shugaban dattawan arewa ne wanda ya rasu a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba yana da shekaru 87.

Tsohon ministan wutar lantarkin da karafunan ya rasu a Jos dake jihar Filato.

6. Demola Seriki

Jakadan Najeriya a Spain, Demila Seriki ya rasu yana da shekaru 63 a ranar Talata, 15 ga watan Nuwamban 2022 a birnin Madrid.

7. Alaafin na Oyo

Sarkin mai daraja ta farko, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya rasu a ranar Juma'a, 22 ga watan Afirilun 2022 yana da shekaru 83 a duniya,

Basaraken kudu maso yamman ya rasu a asibitin koyarwa na jam'iar Afe Babalola dake Ado-Ekiti, jihar Ekiti bayan kwashe sama da rashin karni kan karagar mulki.

8. Olubadan

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban Kasan South Sudan Yana Fitsari A Wando Ana Tsakiyar Taro

Mai martaba, Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji ya rasu yana da shekaru 93 a duniya a ranar Lahadi, 2 ga watan Janairu.

Basaraken ya rasu a matsayinsa na sarki na 41 na tsohon garin Ibadan a asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan dake jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng