2023: Atiku Ya Bukaci Peter Obi Ya Jingine Takara, Ya Koma Jam'iyyar PDP
- Tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ta nemi ɗan takarar LP, Peter Obi ya aje takara ya marawa PDP baya a 2023
- Kakakin PCC, Sanata Dino Melaye, yace Obi ba zai iya cin nasara a zaben da ke tafe ba saboda a iya yanki ɗaya ya yi suna
- Sanatan ya gargaɗi Obi da cewa duk kuri'ar da ya samu naƙasu ce ga ɗan takarar jam'iyyar PDP
Abuja - Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, (PCC) ya yi kira ga mai neman zama ahugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya jingine tikitinsa, ya mara wa Atiku baya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto kwamitin na cewa ɗan takarar jam'iyyar LP bai kai matakin da zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa ba a babban zaɓen da ke tafe.
Mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku Abubakar, Sanata Dino Melaye, shi ne ya yi wannan furucin yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Asabar.
Melaye yace kaɗa wa Obi kuri'a a zaɓen dake zuwa a watan Fabrairu, 2023 babbar naƙasu ne ga Atiku domin zai zama tamkar dangwala wa ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Tinubu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar kakakin PCC, tsohon gwamnan jihar Anambra bai haɗa abubuwan da ake bukata da zasu iya kai shi ga nasara a zaɓe ba, kamr yadda Leadership ta rahoto.
Yan Najeriya ba zasu iya jure wani zangon mulkin APC ba - Melaye
Bisa haka, Sanata Melaye, ya yi kira ga mai rike da tikitin LP ya canza shawara kana ya koma jam'iyyar PDP domin tallafa wa Atiku Abubakar ya ɗare kujera lamba ɗaya.
Yace 'yan Najeriya ba zasu iya jure wa wata sabuwar gwamnatin APC ba. Yace ba wani zakaran yanki guda da zai iya kai bantensa a zaɓen shugaban Najeriya.
"Shi kansa Buhari da ya nemi takara a yanki ɗaya kaye ya sha saboda a lokacin gwarzon yanki ne, a jam'iyyar NNPP, APP da CPC duk kaye ya sha har zuwa lokacin da ya nemi takara a inuwar ƙasa baki ɗaya."
"Saboda haka bisa la'akari da tarihi ya kamata Peter Obi ya gane cewa ba'a taɓa samun mutumin da ya shahara a yanki kuma ya zama shugaban ƙasa ba a Najeriya."
- Dino Melaye.
A wani labarin kuma Bola Tinubu Na Gab da Fara Kamfen, Jam'iyyar APC Ta Yi Rashin Babbar Jigo a jihar Ribas
Tsohuwar shugabar hukumar NDDC data fice APC tun watan Yuli, Ibim Semenitari, ta shiga jam'iyyar PDP a jihar Ribas.
Semenitari, tsohuwar kwamishina a mulkin Amaechi, tace dama PDP ce gidanta na farko a siyasa.
Asali: Legit.ng