Bayan Shugaban BoT Ya Yi Murabus, Kujerar Gwamna Tambuwal Ta Fara Tangal-Tangal a PDP

Bayan Shugaban BoT Ya Yi Murabus, Kujerar Gwamna Tambuwal Ta Fara Tangal-Tangal a PDP

  • Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya sauka da muƙamin shugaban kungiyar gwamnonin PDP
  • Wannan matakin na zuwa ne biyo bayan murabus ɗin shugaban BoT, na ƙasa, Sanata Walid Jibrin, wanda aka maye gurbinsa da Wabara
  • Jam'iyyar PDP na cigaba da kokarin sasanta rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tun bayan kammala zaɓen fidda gwani

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi murabus daga kujerarsa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sakkwato daga arewacin Najeriya, ya sanar da murabus ɗinsa ne a wurin taron kwamitin amintattu (BoT) dake gudana yanzu haka a Abuja.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato.
Bayan Shugaban BoT Ya Yi Murabus, Kujerar Gwamna Tambuwal Ta Fara Tangal-Tangal a PDP Hoto: Aminu Tambuwal/facebook
Asali: Facebook

Tun farko, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa shugaban BoT na ƙasa, Sanata Walid Jibrin, ya sauka daga kan muƙaminsa, lamarin da ya jefa kujerar Tambuwal cikin rashin tabbas

Kara karanta wannan

Yanzun nan: PDP ta fadi matsayar ta kan ko Ayu zai ci gaba da kasancewa shugabanta

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa matakin Sanata Jibrin zai rinjayi gwamna Tambuwal ya sauka daga kujerar shugaban gwamnonin PDP domin ya share hanyar komawar kujerar kudancin Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam'iyyar PDP ta tsunduma cikin rikici tun bayan ayyana Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da kuma zaɓo gwamna Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa.

Tsagin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya cigaba da nanata bukatarsu cewa ya zama wajibi shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorcia Ayu, ya bar kujerarsa a wani ɓangaren kokarin sulhu.

Sai dai a halin yanzu, masu ruwa da tsakin jam'iyya musamman 'yan arewa sun rinjayar da cewa shugaban BoT da Gwamna Aminu Tambuwal, su yi murabus daga muƙamansu domin a baiwa kudu.

Ana kyautata zaton bayan kammala taron kwamitin Amintattu (BoT) a yau Alhamis, kwamitin zartarwa mafi koli na jam'iyyar PDP (NEC) zasu gudanar da na su taron.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Goyi Bayan Babbar Bukatar Gwamna Wike, Sabbin Bayanan Sulhun PDP Sun Fito

Atiku Ya Goyi bayan shugaban PDP ya sauka

A wani labarin kuma Atiku Ya Goyi Bayan Babbar Bukatar Gwamna Wike, Sabbin Bayanan Sulhun PDP Sun Fito

Jigon jam'iyyar PDP yace a halin da ake ciki Atiku ya amince shugaban jam'iyya na ƙasa ya sauka daga kujerarsa.

Katch Ononuju, yace ya kamata Atiku ya tabbatar da ikirarinsa na mai haɗa kai ta hanyar daidaita PDP ta zauna daram cikin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262