Magidanci Mai Mata 4 Da 'Yaya 34 Sun yi Rijistan Zabe, Yace Atiku Duk Zasu Kadawa Kuri'u
- Wani Manomi ya saki hotunan iyalinsa kuma yayi alkawarin Alhaji Atiku Abubakar zasu zaba
- Atiku Abubakar, shine dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP
- Hukumar INEC ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa a watan Febrairu, 2023 idan Allah ya kaimu
Wani Magidanci mai mata hudu da 'yaya 34 ya saki hotunan iyalansa da sukayi katin rijistan zabe kuma ya bayyana mutum 1 da dukkansu zasu kadawa kuri'a a zaben 2023.
Magidancin wanda Manomi ne mai suna Yusuf Babale yana da shekaru 49 a duniya.
Ya bayyana cewa da shi, da matansa hudu, da 'yayansa 34 dukkan dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, zasu kadawa kuri'a a zaben 2023.
A hoton da wani Isreal Bulus ya dora a manhajar Facebook, an ga 'yayan mutumin maza da mata rike da katunan zabensu.
Babale ya bayyana cewa Atiku Abubakar kadai ne wanda zai iya hada kan kasar nan duk halin rashin tsaro da wahala da ake ciki.
Kalli hotunansu:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga karshe Atiku Abubakar ya yi maganar ‘rigimarsa’ da Gwamna Wike a PDP
Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin PDP ya gargadi jagororin jam’iyyar hamayyar game da sakin bakinsu.
The Cable ta kawo rahoto a daren Juma’a, 26 ga watan Agusta 2022 cewa Atiku Abubakar ya bukaci manyan PDP su guji kalaman da za su raba kai.
Ganin yadda wasu ke sakin kalamai a game da abubuwan da ke faruwa a jam’iyya, ga kuma zabe ya karaso, Atiku ya fadawa abokan aikinsa su yi hattara.
A wani jawabi da ya fito daga bakin Paul Ibe, ‘dan takaran shugaban kasar ya nuna cewa babu rabuwar kai tsakaninsa da ‘yan bangaren Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng