Tikitin Musulmi da Musulmi Matsala ne ga Najeriya, Sakatare Kungiyar Kiristocin PFN

Tikitin Musulmi da Musulmi Matsala ne ga Najeriya, Sakatare Kungiyar Kiristocin PFN

  • Kungiyar Kiristocin Pentecostal ta bayyanawa mabiyanta irin mutumin da ya kamata a zaba a zaben 2023
  • Shugaban PFN ya bi sahun sauran shugabannin mabiya addinin Kirista wajen nuna amincewarsu da zabin jam'iyyar APC
  • Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin APC Musulmi ne kuma Abokin tafiyarsa Musulmi ne

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Sakatare Janar na kungiyar Kiristocin Pentecostal Fellowship na Najeriya, Dr Cosmos Ilechukwu, ya bayyana cewa tikitin Musulmi da Musulmi matsala ne ga hadin kai da rana goben Najeriya.

Dr Cosmos ya ce wannan shine matsayar kungiyar yayin hira da manema labarai bayan taronsu a hedkwatar kungiyar ta kasa dake jihar Legas ranar Alhamis, rahoton Punch.

Jagoran
Tikitin Musulmi da Musulmi Matsala ne ga Najeriya, Sakatare Kungiyar Kiristocin PFN

Ya bayyana cewa zaben Musulmi matsayin Shugaban kasa kuma Musulmi ya zama mataimaki kara raba kawunan yan Najeriya zai yi kuma kungiyar Kiristoci CAN ta fada musu wanda zasu zaba, riwayar Tribune.

Kara karanta wannan

Zan gyara fannin ilimi cikin wata shida idan na gaji Buhari, inji wani dan takara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa yace:

"Kungiyar Kiristocin Pentecostal Fellowship ta Najeriya na sake jaddada rashin amincewarta da Tikitin yan addini daya saboda babu adalci kuma haka zai sake tsananta rashin zaman lafiya dake tsakaninmu."
"PFN bata taba goyon bayan wani dan takara ba kuma ba zatayi hakan a zaben 2023 ba. Amma zata cigaba da jan hankulan Kiristoci wajen shiga siyasa ayi da su.:
"Muna kira ga mambobinmu su bi umurnin kungiyar CAN wajen mutumin da ya kamata a zabe."

Zamu Samawa Tinubu/Shettima Kuri'u 1.5M, Yan Arewa Mazauna Legas

A wani labarin kuwa, mutan Arewa mazauna jihar Legas sun bayyana niyyar baiwa Asiwaju Bola Tinubu kuri’u miliyan 1.5 a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa, rahoton The Nation

Wannan ya bayyana ne yayin wani taron kaddamar da Alhaji Sa’adu Gulma, matsayin shugaban jam’iyyar APC na al’ummar Arewa dake tashar Tirela na Oko-Oba Abattoir.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa IBB ya rigamu gidan gaskiya

Sa’adu ya ce zabensa matsayin shugaban al’ummmar Arewa na jihar Legas zai bude kofar alheri ga yan Arewa a jihar sosai.

Ya ce kudirinsa shine tabbatar da al’ummar Arewa sun samarwa Tinubu kuri’u miliyan 1.5 a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel