Jerin sunayen Alkalan kotun koli 14 da suka tuhumci Tanko da shan jar miya shi kadai
A farkon makon nan, alkalan kotun kolin Najeriya sun aikewa Alkalan Alkalai, Ibrahim Tanko Mohammed wasikar kar ta kwana bisa abubuwan dake gudana a babbar kotun Najeriya.
A wasikar da manema labarai suka gani, Alkalan kotun koli 14 sun tuhumci Alkali Tanko Mohammed da gazawa wajen gudanar da ayyukansa matsayin shugaba.
Abubuwan da Alkalan suka lissafa a wasikar sun hada da gidaje, motoci, lantarki, man Gas, yanar gizo a gidajen Alkalai, horo, da rashin wuta a kotuna.
Sun zargeshi da cin karansa ba babbaka yayinda yake hanasu kayan jin dadi.
Alkalan sun ce sau biyu kadai suka je Dubai da Zanzibar a shekarar nan sabanin yadda aka saba.
Sun bukaci Alkali Tanko Mohammed yayi bayanin yadda aka yi da kudaden da kotun ke samu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Zaben Osun: Ba a ga Tambuwal, Wike, Fintiri da sauran gwamnoni ba yayin da PDP ta kaddamar da kamfen dinta
Legit ta tattaro muku sunayen Alkalan kotun koli 14
- Olukayode Ariwoola
- Musa Dattijo Mohammed
- Kudirat Motonmori O. Kekere-Ekun
- John Inyang Okoro
- Chima Centus Nweze
- Amina Adamu Augie
- Uwani Musa Abba-Aji
- Mohammed Lawal Garba
- Helen Moronkeji Ogunwumiju
- Abdu Aboki
- Ibrahim Mohammed Musa Saulawa
- Adamu Jauro
- Tijjani Abubakar
- Emmanuel Akomaye Agim.
Martanin CJN Tanko
Yayin martani a wata takarda, wacce Ahuraka Yusuf Isah, hadiminsa ya fitar a madadinsa, na biyar a daraja a fadin kasar ya bayyana yadda ya yi nasarar tattalar arzikin kotun yadda ya dace.
A takaice dai Tanko ya bayyana cewa, zargin da ake masa ba gaskiya bane, kasar ce take a haka kuma yake tattali tare da mafi da abinda aka bada domin hidindimun da suka dace.
Asali: Legit.ng