Peter Obi ya yi magana kan 'yan siyasa, 2023, da hada-kai da Kwankwaso a NNPP

Peter Obi ya yi magana kan 'yan siyasa, 2023, da hada-kai da Kwankwaso a NNPP

  • Peter Obi ya gabatar da wani jawabi na musamman a taron da cocin RHOGIC suka shirya a Abuja
  • ‘Dan takarar shugaban kasar ya ce mafi yawan wadanda suka shiga siyasa a Najeriya su na da matsala
  • Obi ya nuna babu shakka bangaren jam’iyyar LP su na magana da jam’iyyar NNPP domin a dunkule

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya ce mafi yawan ‘yan siyasan Najeriya ba su cancanta da kujerun da suke kai ba.

Daily Trust ta rahoto Peter Obi a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni 2022 yana mai cewa mutanen da ba su da hankali sun yi dumu-dumu a harkar siyasa.

Tsohon gwamnan na Anambra ya yi jawabi ne a wajen wani taro da kungiyar RHOGIC ta shirya a kan rawar ganin da coci ta ke yi a sha’anin siyasa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

‘Dan takaran na zaben 2023 yake cewa mutane za su cigaba da wahala a kasar nan, muddin ba ayi waje da wadannan ‘mahaukata’ a zabe mai zuwa ba.

“Ba za mu iya kyale wannan tsageranci ya cigaba ba, mutanen Najeriya su karbe iko da kasarsu.”
“Kashi 70% na wadanda suke siyasa a yau, bai dace su shiga harkar ba. Na fada a baya, a Najeriya mahaukata sun karbe iko da sha’anin siyasar kasar.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Peter Obi

Peter Obi
Peter Obi a Akwa Ibom a lokacin ya na PDP Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Wasu ba su da hankali?

Punch ta rahoto Obi yana cewa Najeriya ce kurum kasar da wadanda su ka fi kowa rashin cancanta, suke jagoranci, su na wawurar mahaukatan kudi.

A cewar Mista Obi, sai wanda bai da hankali zai sace Naira biliyan 80 daga cikin kudin da ya kamata ayi wa al’umma aiki da su, ya boye a aljihunsa.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

'Dan siyasar ya ce duk wanda ya saci kudin da ya fi karfin bukatarsa, bai da cikakkiyar lafiya.

NNPP da shirin 2023

Da yake magana a kan yiwuwar wasu ‘yan siyasar dabam da na APC da PDP su karbe gwamnati daga hannun APC da PDP, sai ya ce zabi na wajen jama’a.

Rahoton ya ce Peter Obi ya tabbatar da cewa jam’iyyarsa ta LP ta na tattaunawa da NNPP domin ganin yadda za su hada karfi da karfe a zaben kasa na 2023.

Sai dai Obi bai fadi wanda zai zama ‘dan takara tsakanin shi da Rabiu Kwankwaso ba, amma ya ce addu’a kadai ba za ta iya shawo kan matsalar Najeriya ba.

Ana magana da LP - Kwankwaso

A ranar Juma'ar da ta wuce ne aka ji Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso yace su na a tsakiyar tattaunawa da bangaren ‘dan takarar shugaban kasar.

Saboda tsoron lokaci ya wuce, Kwankwaso na NNPP da LP suka zabi ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na wucin gadi kafin a kammala magana.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Atiku yana ruwa, magoya bayan Wike su na barazana a kan dauko Okowa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng