Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alakanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa
- Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce kiyayyar Buhari ta riga ta makantar da David Oyedepo, mamallakin cocin Living Faith
- Hakan ya biyo bayan caccakar gwamnatin da Oyedepo ya yi tare da cewa ba a taba mulkin kama karya a tarihin Najeriya irin wannan cike da almundahana ba
- A cewar faston, "Odita-janar" ya sunkuce N80 biliyan bayan yaran talakawa sun tsaya da karatu, lamarin da yasa Adesina yace tsabar kiyayya ta hana shi tantance labarin
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce David Oyedepo, mai majami'ar Living Faith ta duniya, ya "makance da kiyayyar" da yake wa shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Adesina ya fadi hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Talata.
Yayin jawabi ranar Litinin a wata majami'a, Oyedepo ya siffanta gwamnatin Buhari a "wacce ta fi kowacce zalunci da zalama" a gaba daya tarihin Najeriya.
Ya zargi gwamnatin da nuna halin ko in kula game da walwalar 'yan kasa, musamman dalibai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika, ya kafa hujja da tuhumar akawu-janar na tarayya bisa zarginsa da almundahanan N80 biliyan, inda ya cigaba da cewa da an yi amfani da wannan kudin wajen biya wa kungiyar malamai masu koyarwa na jami'a (ASUU) bukatarsu.
"Dalibai da dama sun aje karatu. Babu kudin biya don ganin an maida su makaranta. Muna ganin yadda ake dauki ba dadi kan taimakawa yara su gama makaranta. Daliban da suka gama da matakin digirin da yafi kowanne daraja ba za su iya samun N30,000 daga azzalumar gwamnati mai cike da son kai da son zuciya," a cewar Oyedepo.
"Wai hakan ne yaki da almundahana. Duk an yaudare ku. Ba yadda za a yi kana rashawa kace za ka yaki rashawa - Wannan shi ne mulkin da yafi ko wanne rashawa a tatihin Najeriya.
"Kuna jin yadda Odita-janar ya sunkuce N80 biliyan. Gaba daya abun da ya dace shi ne a biya jami'oi don su koma bai kai N80 biliyan ba. Sun damu ne? Bai shafi yaransu ba."
Yayin martani, Adesina ya bukaci Oyedepo da yaje ya san bambanci tsakanin Odita-janar da akawu-janar.
"Faston Ota bai ma san abun da yake fadi ko daidai bane. Ya makance da kiyayyar PMB, ya ce Odita-janar ya sace N80 biliyan. Abun kunya! Bai ma san bambanci tsakanin akawu-janar (wanda ake zargi) da Odita-janar ba. Kamar yadda OBJ ya ce tun da dadewa, ya kamata mu dinga sa fastocinmu kan hanya," ya rubuta hakan a shafinsa na Twitter.
Asali: Legit.ng