Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta dare gida biyu bayan sanar da Lawan a matsayin ɗan takara

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta dare gida biyu bayan sanar da Lawan a matsayin ɗan takara

  • Jam'iyyar APC fara tarwatse wa biyo bayan ayyana Sanata Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar shugaban kasa ta maslaha
  • Sanata Abdullahi Adamu ya gaya wa sauran mambobin kwamitin NWC batun Lawan amma nan take suka yi fatali da shi
  • Sakataren tsare-tsare ya ce ba su da wani zaɓi da ya zarce bin bayan matsayar gwamnonin APC na kai takara kudu

Abuja - Mambobin kwamitin gudanarwa NWC na jam'iyyar APC ta ƙasa sun rabu gida-gida kan zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na maslaha.

Punch ta rahoto cewa mambobin NWC sun gana ranar Talata domin biyayya ga umarnin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na cewa ya kamata a zaɓi magajinsa ta hanyar sulhu.

Snaata Ahmad Lawan.
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta dare gida biyu bayan sanar da Lawan a matsayin ɗan takara Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa yayin taron, an sanar da wani ɗan takara da sunan shi ne zaɓin shugaba Buhari, amma mambobin NWC suka yi watsi da shi nan take.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC ta karyata zaban Lawan a matsayin ɗan takarar Maslaha

Wani mamba a kwamitin NWC ya shaida wa wakilin jaridar cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, aka sanar musu da sunan ɗan takarar maslaha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan ya sa wasu mambobin kwamitin NWC suka yi watsi da lamarin sakamakon haka aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin su.

Muna goyon bayan gwamnoni - NWC

Mambobin kwamitin gudanarwa NWC na APC sun bayyana cewa suna bayan matsayar gwamnoni na kai takara kudancin Najeriya.

Sakataren tsare-tsare na APC, Sulaiman Argungu, yace Sanara Adamu ya sanar da su batun zaɓen Lawan a matsayin ɗan takarar maslaha.

Sai dai a cewarsa Shi da takwarorinsa na NWC suna tare da matsayar gwamnonin arewa, wanda gwamnonin kudu suka amince da shi.

A Wani labarin kuma Fadar shugaban ƙasa ta maida wa Tinubu martani kan taimaka wa Buhari a 2015

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan dan takarar da yake so ya gaje shi

Fadar Shugaban kasa ta ce babu wani mutum ɗaya da zai bugi kirjin shi ya ce shi ya kai Buhari ga nasara a shekaru Bakwai da suka wuce

Yayin raddi kan ikirarin Bola Tinubu a wata sanarwa, fadar shugaban ta ce miliyoyin yan Najeriya ne suka kaɗa wa Buhari kuri'un su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262