Yanzu-yanzu: Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP
- Bayan sa'o'i sama 15 da deleget suka taru a farfajiyar Velodrome na filin kwallon Abuja, an sanar da sakamako
- Alhaji Atiku Abubakar ya samu gagarumar nasara kan Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike
- Sauran yan takaran da suka dan tabuka kokarin sune Bukola Saraki, Emmanuel Udom da Bala Mohammed
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar People's Democratic Party PDP.
Kamar yadda yayi a 2019, Atiku yanzu shine zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Atiku ya lallasa yan takara 12 da suka fafata a zaben inda ya samu kuri'u 371
Wanda ya zo na biyu shine Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike wanda ya samu kuri'u 237.
Sannan Bukola Saraki wanda ya samu kuri'u 70.
Shugaban kwamitin zaben, Sanata David Mark, ya sanar da haka a karshen kirgen.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ga jadawalin sakamakon:
Sunayen yan takara | Adadin Kuri'in da suka samu |
Tari Oliver Diana | 1 |
Sam Ohabunwa | 1 |
Pius Anyim | 14 |
Udom Emmanuel | 38 |
Bala Mohammad | 20 |
Bukola Saraki | 70 |
Nyesom Wike | 237 |
Atiku Abubakar | 371 |
Dele Momodu | 0 |
Ayo Fayose | 0 |
Adadin kuri'un da aka kada | 763 |
Adadin kuri'u masu kyau | 751 |
Adadin kuri'un da aka watsar | 12 |
Tarihin takarar Shugaban kasa da Atiku Abubakar ya yi
A baya, mun tattaro lokutan da Atiku Abubakar ya nemi kujerar shugaban kasar Najeriya a babban zabe ko zaben fitar da gwani, ko akalla ya yi niyyar neman mulki.
1. Zaben 1999
Atiku Abubakar ya nemi ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar SDP a zaben 1999 bayan an haramtawa su Janar Shehu Musa ‘Yar’adua shiga siyasa.
Irinsu Shehu ‘Yar’adua sun marawa Atiku baya a zaben tsaida ‘dan takara da aka shirya a Jos, amma sai ya zo na uku a bayan MKO Abiola da Babagina Kingibe.
2. Zaben 2003
Ana tunanin cewa Atiku Abubakar ya yi yunkurin neman tikitin jam’iyyar PDP a zaben 2003, amma mai gidansa a lokacin, Olusegun Obasanjo ya shawo kansa.
Bayan shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya samu tazarce, sabani ya shiga tsakaninsa da Atiku.
3. Zaben 2007
A karshe dole Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP a dalilin rigimarsa da shugaba Obasanjo, ya shiga ACN kuma ya samu tikitin takarar shugaban kasa
A babban zaben 2007 Atiku ya zo na uku ne bayan Ummaru ‘Yar’adua da Muhammadu Buhari.
4. Zaben 2011
A zaben da aka yi a shekarar 2011 ba a bar Atiku Abubakar a baya ba. Babban ‘dan siyasar ya gwabza da shugaba mai-ci Goodluck Jonathan wajen samun tikitin PDP.
A karshe dai Goodluck Jonathan ya lashe zaben fitar da gwanin da jam’iyyar PDP ta shirya, kuma ya yi nasara a babban zabe inda ya doke irinsu jam’iyyun CPC da ACN.
5. Zaben 2015
Daga baya Atiku ya sake barin PDP a wani karon, ya shiga sabuwar jam’iyyar APC da aka kafa da nufin ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2015, amma bai dace ba,
A zaben tsaida ‘dan takara da jam’iyyar APC ta shirya a Legas a Disamban 2014, Atiku Abubakar ya zo na uku ne – bayan Muhammadu Buhari da Rabiu Musa Kwankwaso.
6. Zaben 2019
Har ila yau Atiku Abubakar bai hakura a 2019 ba, da shi aka nemi tutar PDP a garin Fatakwal inda ya doke su Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da Kwankwaso, da sauransu.
A babban zaben da aka shirya, Atiku da jam’iyyar PDP sun sha kashi a hannun Muhammadu Buhari na APC mai mulki. An ba PDP ratar kuri'u fiye da miliyan uku a zaben.
Asali: Legit.ng