Zaben 2023: Yadda tsoron Atiku Abubakar ya jefa Jam’iyyar APC a cikin tsaka mai-wuya
- All Progressives Congress ta ki ayyana yankin da zai fito da ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023
- Jam’iyya mai mulki ta shiga rububi ne saboda tsoron PDP za ta iya tsaida irinsu Atiku Abubakar
- Tsoron da shugabannin APC su ke yi shi ne rasa kuri’un yankin Arewa idan aka ba ‘Dan kudu tikiti
FCT, Abuja – Wani rahoto da ya fito daga Punch a karshen makon nan ya bayyana dalilin jam’iyyar APC na kin fadin yankin da za ta kai takara.
Saura makonni biyu a gudanar da zaben fitar da gwani a jam’iyyar APC, amma har yanzu ba a tantance daga inda ‘dan takarar shugaban kasa zai fito ba.
Jaridar ta ce alamu na nuna cewa jam’iyyar PDP za ta tsaida ‘dan Arewa ne a matsayin wanda zai rike mata tuta a zaben da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu.
A halin da kasar ta ke tafiya, ana tunanin mafi yawan mutane za su zabi ‘dan takararsu a zaben 2023 ne la’akari da addininsa, kabilarsa, da ma inda ya fito.
Wata majiya a APC ta shaidawa jaridar cewa za a bar kofar neman shugaban kasa ne a bude.
“Bai cikin tsarin mulkin mu cewa a hana wasu damar da doka ta ba su. Sannan kundin tsarin mulki ya ce kowa zai iya neman mulki.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A 2014, Rochas Okorocha ya yi takara da mutane hudu daga Arewa. A 1999, Alex Ekwueme da Abubakar Rimi sun yi takara da Obasanjo.”
“Saboda haka ba zai yiwu a ce an sabawa dokar da tun farko babu ita ba. Babu wanda zai kama mu da laifin saba wata dokar da ba ayi ta ba.”
- Majiyar APC
Takarar Bola Tinubu
Har ila yau, majiyar ta na ganin idan Atiku Abubakar aka tsaida a matsayin ‘dan takarar PDP, to jam’iyyar APC za ta fuskanci barazana a zabe mai zuwa.
Da aka tambaye shi a game da takarar Bola Tinubu, sai ya ce idan shi ya lashe zaben fitar da gwani, watakila za su iya yin tikitin Musulmi da Musulmi.
“Idan ‘Dan Arewa bai samu tuta a APC ba, to dole ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa ya zama musulmi mai karfi daga yankin Arewacin Najeriya.”
- Majiyar APC
Idan tsohon gwamnan na Legas da musulmin Arewa suka tsaya, ana ganin jam’iyyar APC mai mulki za ta yi nasara a kasar Hausa da kudu maso yamma.
Tein Jack-Rich ya fito a APC
Tein Jack-Rich ya shiga takarar 2023 a karkashin APC. Ku na da labari Atajirin ya nada tsohon gwamna Isa Yuguda ya zama shugaban yakin neman zabensa.
Da yake jawabi, Jack-Rich ya sha alwashin habaka tattalin arzikin Najeriya ba tare da cin bashi ba. Rich yana cikin masu kananan shekarun da ke yin takaran.
Asali: Legit.ng