Gwamnan APC ya yi magana kan zargin 'cin amanar' Tinubu saboda zai yi takara da shi
- Gwamnan jihar Ekiti ya yi karin-haske a kan takarar shugabancin Najeriya da yake shirin yi a APC
- Dr. Kayode Fayemi ya ce neman tikitin jam’iyyar APC ba yunkurin juyawa Bola Tinubu baya ba ne
- Shugaban kungiyar NGF ya bayyana cewa kujerar shugaban Najeriya ba sarautar gargajiya ba ce
Abuja - Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi ya musanya zargin da aka yi masa na cewa yana neman juyawa Asiwaju Bola Tinubu baya saboda zai yi takara.
Dr. Kayode Fayemi ya yi magana ne game da burin takara da yake yi a APC lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Laraba.
Ana ganin cewa Bola Tinubu tsohon ubangida ne ga Kayode Fayemi, wanda yanzu yake tunanin wuyansa ya yi kwarin da zai iya yin takara da Tinubu.
Shugaban gwamnonin kasar yake cewa tsohon gwamnan na Legas ba zai dauki neman takara da shi a APC a matsayin butulci ko kokarin juya masa baya.
Abin da Fayemi ya fada
“Asiwajun da na sani kuma na zauna da shi ba zai yarda a bata sunan kowa ba. Ban yarda zai yi amfani da kalmomi irinsu ‘cin amana.’”
“Ba gado ba ne; ba wata sarautar gargajiya mu ke nema ba. Ofishin da mu ke nema na wanda zai canza rayuwar mutanen Najeriya ba”
“Magana ce ta Najeriya, abin da ya hada dukkanin ‘yan Najeriya.” – Kayode Fayemi.
Takarar Fayemi a APC
Legit.ng ta ce gwamnan ya bayyana cewa shigarsa takara zai kawo juyin juya-hali a Najeriya.
Shigan Kayode Fayemi takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa ya sa masu neman tikiti a jam’iyyar APC daga bangaren kudu maso yamma sun karu.
Baya ga Gwamnan jihar Ekiti, Bola Tinubu zai fuskanci kalubale daga tsofaffin yaransa; Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon gwamna Sanata Ibinkunle Amosun.
Kowane daga cikinsu ya na so ya gaji kujerar Mai girma Muhammadu Buhari a zaben 2023. Duk wanda ya samu nasara zai kara da PDP da sauran jam'iyyu.
Shekaru 12 da mutuwar Yar'adua
A yau da safe aka ji labari Goodluck Ebele Jonathan ya rubuta ta’aziyya mai ban tausayi, yana tunawa da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’Adua.
Marigayi Umaru Yar’Adua ya rasu ne a irin wannan rana a shekarar 2010 bayan ya yi ta fama da rashin lafiya. Marigayin ya yi shekaru yana mulkin Najeriya.
Asali: Legit.ng