2023: An rabawa Gwamna hankali a APC, a karshe ya zabi Osinbajo a kan Bola Tinubu

2023: An rabawa Gwamna hankali a APC, a karshe ya zabi Osinbajo a kan Bola Tinubu

  • Da alamu Gwamnan jihar Ogun ya yi zabi tsakanin Farfesa Yemi Osinbajo da Bola Ahmed Tinubu
  • Yemi Osinbajo da Bola Ahmed Tinubu duk su na shirin yin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC
  • Da Osinbajo ya ziyarci Ogun, Gwamnan ya shaidawa Duniya cewa zai goyi bayansa ne a zaben 2023

Ogun - A ranar Talata, 26 ga watan Afrilu 2022, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana cewa zai marawa Yemi Osinbajo baya a zabe mai zuwa.

Daily Trust a wani rahoto da ta fitar, ta ce an sa Dapo Abiodun a tsaka mai wuya wajen zaben wanda zai goyi baya ya zama ‘dan takarar shugaban kasa.

Mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo yana neman tikiti, haka zalika Bola Ahmed Tinubu ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Osinbajo ya yi karin-haske kan dalilin yin takara, yace akwai sirrin da shi kadai ya sani

Rahoton ya ce Farfesa Osinbajo da tsohon mai gidansa Tinubu sun taimakawa Abiodun wajen zama gwamna a lokacin da yake rikici da Ibikunle Amosun.

Abin da ya faru a 2019

Sanata Ibikunle Amosun ya marawa Abdulkabir Akinlade baya ne a zaben gwamnan Ogun a 2019. Amma a karshe Dapo Abiodun ne ya samu nasara a APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa abin da ya faru a zaben 2019 ya rabawa gwamnan hankali, Kowane bangare yana ganin ya kamata gwamna ya yi hallaci.

Ana kamfe a Ogun
Buhari, Osinbajo da 'Yan APC ana kamfe Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Hakan ta sa mukarrabai da hadiman gwamnan na jihar Ogun suka rabu biyu, wasu su na tare da Osinbajo, sauran kuma sun zabi su bi Bola Tinubu sau da kafa.

A ranar Talatar nan Mai girma gwamna Abiodun ya ce zai goyi bayan mataimakin shugaban kasa ne wanda mahaifarsa ita ce garin Ikenne a jihar da yake mulki.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Cigaban gwamnatin Buhari

Premium Times ta ce da yake magana a fadar wasu Sarakuna, gwamna Abiodun ya ce zaben Osinbajo a 2023 zai sa a cigaba da ayyukan Muhammadu Buhari.

Abiodun ya ce Farfesa Osinbajo ya taimaka sosai wajen nasarorin da gwamnatin APC ta samu a shekaru bakwai, don haka yake ganin ya dace ya karbi shugabanci.

An ji Abiodun yana yabon gaskiya, kwarewa da mutuncin mataimakin shugaban kasar, ya tabbatar masa cewa za su mara masa baya a zaben shekara mai zuwa.

Takarar Jonathan a APC

A makon nan aka ji labari Gwamna Ben Ayade ya yi magana a kan takarar Goodluck Jonathan a jam’iyyar APC, ya ce ba zai kalubalci Jonathan idan ya samu tikiti ba.

Farfesa Ayade bai je fadar Aso Villa da niyyar shiga takara ba, a cewarsa sai Muhammadu Buhari ya umarce shi da ya jarraba sa’arsa a zaben fitar da gwanin da za ayi.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng