Matashin da zai yi takarar Shugaban kasa a APC, ya nemi ayi masa karo-karon kudin fam
- Adamu Garba ya nuna da gaske yake yi wajen neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki
- Duk da jam’iyyar ta tsawwala kudin fam, Malam Adamu Garba II sam bai da niyyar hakura da burin na sa
- Matashin ‘dan siyasar ya fito Facebook da Twitter ya bada lambobin akawun domin karbar gudumuwa
Malam Adamu Garba II ya fara yakin neman zaben shugaban kasa gadan-gadan, ya yi kira ga mutane su taimakawa wannan tafiya da ya dauko.
Legit.ng Hausa ta fahimci Adamu Garba II ya saki lambobin akawun na banki ga masoyansa domin a taimaka masa da kudin da zai yanki fam a APC.
Garba ya ce duk da fam din takarar shugaban kasa a APC ya yi tsada, ba zai karaya da yin takara ba, domin ya nuna cewa irinsa sun damu da kasar nan.
Bayan ya rubuta sakon bara a Facebook, Garba II ya rubuta irin makamancin wannan a Twitter.
“Ya ku mutanen Najeriya. Na soma wannan tafiyar. Ga wadanda suka yi alkawarin bada gudumuwa, ga lambar akawun nan.”
“1008404148 | Bankin Zenith. Ba a duba kafin a tsaida kudin fam a N100m ba.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Amma hadin-kan da za mu yi wajen bada gudumuwar nan zai nuna da gaske mu ke yi, mun damu da halin da Najeriya ke ciki.”
“Mu na bada shawarar ku hada da lambarku wajen turo kudin, ko kuma kira wadannan lambobin:
09034766771
08133068988
08060183701
Za kuma ku iya kiran wadannan lambobi da ke sama domin ka bada gudumuwarku.
Nagode.”
Martanin mutane a Facebook
Irinsu Abdussalam Muhammad Kazeem sun ce Allah dai ya bada sa’a, amma ba da su ba. Shi kuma Abdussalam Abdullahi ya ce tamkar a ba APC kyauta ne.
Wallahi gara kuɗin su zube ɓarawo ya tsinta.
- Sada Suleiman Usman
Akalla kafin ka bada lambar akawun, sai ka fada mana nawa ka ke da shi tukuna a kasa.
- Husaina Sufyan Ahmed
Ka fara bara ne. Idan ka samu, wa zaici Kudin? Hauka akeyi aka ce maka.
- Najeeb Nobel
Baba Buhari ya Sha mu, mun warke. Idan mun hada maka Kudin form yaya zaka Yi da delegates?
- Sani Labaran
Za mu bada gudumuwa
Allah Ya Tabbatar Da Alkhairi. Za Mu Yada; Za Mu Saka - Insha'Allahu.
- Muhammad Bashir
Allah Ya Tabbatar Da Alkhairi. Za Mu Yada; Za Mu Saka - Insha'Allahu.
- Abdullateef Hamza
Asali: Legit.ng