Da duminsa: Wani attajiri dan jihar Kebbi ya zuge N100m don sayawa Tinubu Fom din takara

Da duminsa: Wani attajiri dan jihar Kebbi ya zuge N100m don sayawa Tinubu Fom din takara

  • Farawa da iyawa, wan mutum guda ya ce zai sayawa Tinubu fom din takara kujerar shugaban kasa
  • Wannan na zuwa ne yan sa'o'i bayan jam'iyyar All Progressives Congress APC ta sanar da farashin Fom
  • Asiwaju Bola Tinubu ne mutum na farko da ya fara alanta niyyar gajen shugaba Buhari

Attajirin dan kasuwa dan jihar Kebbi, Aminu Sulaiman, ya zuge cheque na milyan dari don sayawa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu tikitin takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC.

Aminu Sulaiman, wanda shine Dirakta Janar kungiyar goyon bayan Tinubu watau Tinubu Support Organisation (TSO).

Ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin Laraba, 20 ga watan Afrilu, 20202

Yace:

"Ni Hanarabul Aminu Suleiman (D.G TSO) na rubuta cheque na naira milyan 100 don sayar Fom din takara wa shugabanmu Asiwaju Bola Tinubu."

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na fitar da N100m don sayawa Tinubu fom din takara, Attajirin Dan kasuwa

APC ta sanar da farashin da zata sayar da fam ga duk wadanda ke son takarar

APC ta ce naira milyan dari kowani dan takaran shugaban kasa zai biya don yankan Fom.

Na gwamna kuwa, za'a sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata zasu kashe N20m.

N10m za ta sayar da Fam ga masu neman kujerar yan majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.

Za'a fara sayar da Fam din daga ranar 22 ga Afrilu, 2022.

Bayan sanar da farashin, jam'iyyar APC ta ce duk matashi mai kasa da shekaru 40 a duniya an yi masa rahusa ya biya rabin kudin fam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng