APC ta soki Osinbajo don zai yi takara da Tinubu, ta ce bai tsinana komai ba a shekara 7

APC ta soki Osinbajo don zai yi takara da Tinubu, ta ce bai tsinana komai ba a shekara 7

  • Jam’iyyar APC ta yi wa Yemi Osinbajo kaca-kaca ganin ya yarda ya goge raini da Bola Tinubu a 2023
  • Kakakin APC na jihar Legas ya ce a filin zabe, za a ga iya abin da Farfesa Yemi Osinbajo zai tabuka
  • Seye Oladejo ya soki Farfesa Osinbajo, har yana zargin bai yi abin kirki a kujerar da yake kai ba

Lagos - Mai magana da yawun jam’iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Legas, Seye Oladejo, ya soki mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Jaridar Premium Times ta ce Seye Oladejo ya caccaki Farfesa Yemi Osinbajo ne saboda ya ayyana niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin APC.

A wani jawabi da ya fitar, Oladejo ya bayyana cewa Farfesa Osinbajo ya na da dama a matsayinsa na ‘dan kasa ya fito takara, amma sai ya nuna ba zai ci zaben ba.

Kara karanta wannan

Abin da ‘Yan Facebook, Twitter ke ta fada kan shirin takarar Osinbajo a zabe mai zuwa

Kakakin jam’iyyar ta APC na reshen jihar Legas ya ce sun san da take-taken Osinbajo, abin da su ke bukata shi ne ‘yan siyasa su hadu a wajen zaben tsaida gwani.

A cewar mai magana da yawun na APC, da ya kalli bidiyon da aka yi a cikin daki, bai fahimci jawabin tsayawa takara mataimakin shugaban kasar yake yi ba.

Rahoton ya ce Oladejo ya na ganin kwararren 'dan siyasa APC ta ke bukatar ta tsaida, ya na nuni ga Tinubu.

Osinbajo da Tinubu
Farfesa Osinbajo da Bola Tinubu Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

“Babu matsala. Mun san cewa zai ayyana niyyar takara. Su kyale mu ayi zaben fitar da gwani. Ya zo, ya (Osinbajo) gwabza da Asiwaju (Bola Tinubu).”
“Sam ban damu ba. Mun fahimci ya na da damar da zai yi takara a tsarin mulkin kasa. Mun lura da yadda ya gagara yin abin kirki a shekaru takwas.”

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya bayyana abin da zai tarwatsa Jam’iyyar adawar a zaben Shugaban kasa

Ashe jawabin ayyana takara ne?

“Na yi tunanin makoki nake sauraro, sai can na gane cewa jawabin tsayawa takara ne a cikin daki. ‘Yan Najeriya za su yi masa hisabi idan lokaci ya zo.”
“Iya sani na, mataimakin shugaban kasa ne yake kula da tattalin arzikin Najeriya.”
“Abin da kurum mu ke bukata shi ne ayi zaben fitar da gwani. Sai mu ga irin goyon bayan da Osinbajo zai samu daga ‘ya ‘yan jam’iyya (APC).
Wannan mutumin ne da ya gagara lashe akwatin zabensa. Bani da wani labarin cewa abubuwa sun canza daga zaben da aka yi karshe zuwa yanzu.”

- Seye Oladejo

'Yan takara 35 sun fito takara

Dazu kun ji cewa idan aka cire Atiku Abubakar, akwai sama da mutum 16 da ke neman tikitin PDP, a APC kuwa su Farfesa Yemi Osinbajo za su kara da Bola Tinubu.

Nonye Josephine Ezeanyaeche ‘yar shekara 102 ita ce mafi tsufa a ‘yan takaran 2023, Chukwuka Monye mai neman tikitin ADC ya na cikin ‘yan auta a shekara 42.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa: Yadda Farfesa Yemi Osinbajo zai ayyana shirin gaje kujerar Buhari a yau

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng