Shehu Sani ya fadi gaskiyar yadda ya samu fam din neman takarar Gwamnan Kaduna a PDP
- ‘Danuwan Marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya shiga cikin masu son takarar gwamna a Katsina
- Arc. Ahmed Aminu Yar’Adua zai nemi kujerar Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar PDP
- A jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya biya kudi sama da Naira miliyan 20 ya saye fam din shiga zabe
Katsina - Wani ‘danuwa a wajen Marigayi Umaru Musa Yar’Adua watau Arc. Ahmed Aminu Yar’Adua ya na so ya yi takarar gwamna a jihar Katsina.
Daily Trust ta ce Arc. Ahmed Aminu Yar’Adua ya karbi fam din shiga takara, ya na mai sa ran samun tikitin jam’iyyar hamayya ta PDP a zabe mai zuwa.
Aminu Yar’Adua da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Yar’Adua, kakansu daya. Marigayi Yar’Adua ya yi gwamna a Katsina tsakanin 1999 da 2007.
Da yake jawabi bayan ya karbi takardar shiga neman takara, Arc. Aminu Yar’Adua ya shaida cewa zai yi kokarin kawo gyara idan ya samu mulki a Katsina.
‘Dan siyasar da ya rike shugaban hanyoyin ruwa na kasa watau NIWA ya ce gwamnatin Aminu Masari ta jefa jiharsu a cikin wani irin mummunan yanayi.
A wani kaulin, Yar'Adua ya sha alwashin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ya addabi Katsina.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2023: Siyasar jihar Katsina
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sauran wadanda ake tunanin za su nemi takara a PDP sun hada da Lado Danmarke, Salisu Majigiri, da Muttaqa Rabe Darma.
A jam’iyyar APC kuma Mustapha Inuwa, Dikko Radda, Ahmed Babba-Kaita, Manir Yakubu, Ahmed Dangiwa duk sun kwallafa rai a kan tikiti a zaben 2023.
Shehu Sani ya saye fam a PDP
A daidai wannan lokaci kuma Shehu Sani ya na yankan fam din neman takarar gwamna a Kaduna.
Tsohon ‘dan majalisar na Kaduna ta tsakiya ya ce zai nemi kujerar gwamna ne domin zai iya shawo kan matsalolin jihar Kaduna, musamman rashin tsaro.
Sanata Sani ya tabbatar da wannan a shafinsa na Twitter a jiya, ya bayyana cewa da kudinsa ya saye fam din, ba yadda wasu ‘yan siyasan suke yawan fada ba.
“Na karbi fam din takarar gwamna…ba wata kungiya ta saya mani ba…ba zan sharba karya ba.” - Sanata Shehu Sani
Masu karyar an saya masu fam
Kwanakin baya ne tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce ‘yan Najeriya su raba kansu da zaben masu neman takarar da suke yi wa jama’a karya.
Cif Obasanjo ya yi kira ga al’umma su guji kada kuri’a ga duk 'dan siyasar da ke da'awar wasu suka saya masa fam din takara domin ya nuna ya na da masoya.
Asali: Legit.ng