Tsohon Gwamnan PDP ya ajiye aikin da aka ba shi a PDP, zai fito neman takara a zaben 2023
- Ayodele Peter Fayose ya yi murabus daga kwamitin PDP na kason kujerun siyasa a zabe mai zuwa
- Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya dauki wannan mataki ne domin ya na da niyyar yin takara a 2023
- Tun da har ya na harin kujera, Fayose ya na ganin bai kamata ya zama cikin ‘yan kwamitin nan ba
Lagos - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya fice daga kwamitin da jam’iyyar PDP ta kafa domin duba yadda ya kamata ayi rabon mukamai a 2023.
Rahoton da The Cable ta fitar a ranar Talata, 5 ga watan Afrilun 2022 ya nuna Ayodele Peter Fayose ya bada wannan sanarwa ne a wasikar da ya aika.
Ayo Fayose ya fitar da takarda yana mai sanar da shugaban kwamitin, Gwamna Samuel Ortom cewa ya cire kan shi daga cikin ‘ya ‘yan kwamitin na sa.
Dalilin ‘dan siyasar na daukar matakin shi ne zai nemi takarar shugaban kasa a zaben 2023, don haka yake ganin son zuciya ne ya cigaba da wannan aikin.
Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan wasika da Fayose ya rubuta daga gidansa da ke Legas. Rahoton ya ce Fayose ya yaba da irin kokarin 'yan kwamitin.
“Ina rubuta wannan ne domin in godewa jam’iyya da daukacin ‘yan kwamitin nan. Ina godiya ga dattaku, hidima, da kishinku ga jam’iyya da kasarmu.”
“Ganin yadda kuka yi wannan aiki mai wahalar sha’ani, na raba kujerun siyasa da mukamai, musamman na kujerar shugaban kasa a cikin natsuwa.”
“Ina addu’a sakamakon aikin na ku ya kawo fahimtar juna, zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali da jam’iyyarmu da daukacin kasarmu baki daya.”
“A zaman karshe, na kyankyasa niyyar neman tikitin takarar shugaban kasa a zaben fitar da gwani da babban zabe, ba daidai ba ne in shiga wannan aiki.”
“Saboda haka, jihata ta bada sunan Dr. Gbenga Faseluka domin ya maye gurbi na.” - Ayo Fayose.
Fayose ya lashe amansa kenan?
Kwanakin baya ne aka ji labari cewa a zaben 2023 da ake shirin yi, kamar Ayodele Peter Fayose ya na tare da Nyesom Wike wajen samun tikitin jam’iyyar PDP.
Fayose ya bayyana cancantar gwamna Wike da yin takara a 2023. Har an ji Fayose ya na cewa zai maidawa wanda suka sayawa Wike fam kudin da suka kashe.
Asali: Legit.ng