Yanzu-yanzu: PDP tayi watsi da tsarin karba-karba, tace kowa zai iya takaran kujeran shugaban kasa

Yanzu-yanzu: PDP tayi watsi da tsarin karba-karba, tace kowa zai iya takaran kujeran shugaban kasa

Kwamitin yanke shawara kan tsarin karba-karban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) yi watsi da tsarin kuma tace kowa na iya takaran kujeran shugaban kasa.

Kwamitin karkashin jagorancin Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce kowani mutum daga kowani yanki zai iya yankan tikitin takara karkashin lemar PDP.

PDP ta yi wannan sanarwa ne ranar Talata, 5 ga watan Afrilu bayan ganawar kwamitin a hedkwatar da jam'iyyar dake Abuja.

Saurari karin bayani...

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng