Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

  • Kan wadanda ke neman tikitin shiga takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya rabu uku zuwa yanzu
  • An samu akalla bangarori uku da suke da mabanbantan ra’ayi a game da yankin da za a kai takara
  • Akwai masu ganin a bar kofa a bude, akwai masu cewa a kai takara kudu, akwai wasu a gefe dabam

Nigeria - Yakin neman zaben shugaban kasa ya raba babbar jam’iyyar hamayya watau PDP zuwa bangarori uku. The Nation ta fitar da wannan rahoto a yau.

Kamar yadda mu ka samu labari, rabuwar kan ya bayyana a jam’iyyar PDP ne saboda gardamar da ake yi a game da yankin da za a ba tikitin shugaban kasa.

A tsagin farko akwai Atiku Abubakar wanda a wannan karo ma yake neman PDP ta sake ba shi takara. Atiku ya nemi wannan kujerar sau biyar a tarihinsa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya ya fadawa ‘Yan Najeriya su kauracewa zaben Atiku, Tambuwal, Saraki da Obi

Rahoton ya ce gwamnan jihar Adamawa (inda Atiku ya fito), Ahmadu Umaru Fintiri ya na tare da shi. Haka zalika gwamnan jihar Edo watau Godwin Obaseki.

Tsagin Bukola Saraki

A bangare na biyu akwai wasu ‘yan takara daga Arewa da suke goyon bayan su hada-kai domin a fito da mutum daya daga cikinsu, wanda za a gwabza da shi.

Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ya na tare da gwamnonin Bauchi da Sokoto; Bala Mohammed da Aminu Waziri Tambuwal a rukunin nan.

'Yan takarar PDP 3
Wasu manyan masu takara a PDP Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Bangare na uku su ne ‘yan siyasar da ke ganin cewa ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya.

"'Yan kudu su karbi mulki"

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya na cikin masu wannan ra’ayi. Daga cikin masu goyon bayan hakan akwai gwamnonin kudancin Najeriya da-dama.

Kara karanta wannan

Gardamar yankin da za a ba takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya kawo rigima a PDP

Wadanda suka yi fice a cikinsu sun hada da Ifeanyi Ugwuanyi, Okezie Ikpeazu, Seyi Makinde da kuma gwamna Samuel Ortom wanda shi ya fito ne daga Arewa.

Wani ‘dan siyasar Arewa da ke da wannan ra’ayi shi ne tsohon gwamnan Benuwai, Gabriel Suswam. Sanata Suswam yana cikin wadanda ke tare da Wike.

Sawun keke

Akwai masu neman takarar da ba a san inda suka sa gaba ba tukuna. Daga cikinsu akwai Dele Momodu, Mazi Sam Ohuabunwa da gwamna Udom Emmanuel.

Ina Anyim Pius Anyim ya dosa?

Shi dai Anyim Pius Anyim ya na cikin masu ganin ‘dan kudu ya kamata ya karbi mulki a 2023.

Kwanakin baya aka ji cewa tsohon shugaban majalisa, Sanata Anyim Pius Anyim ya ziyarci jihar Filato a yunkurinsa na ganin ya zama ‘dan takarar PDP a 2023.

Anyim Pius Anyim wanda ya na cikin masu harin takarar shugaban kasa ya na ganin ya kamata a dauko mutumin Kudu a 2023 ne idan da adalci a jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng