Rigingimu na neman ratsa PDP, ‘Ya ‘yan Jam’iyya su na zargin shugabanninsu da zagon-kasa
- ‘Ya ‘ya da shugabannin jam’iyyar PDP sun samu kan su a cikin sabani a wasu jihohin kasar nan
- Masu ruwa da tsakin PDP a jihar Anambra sun kai kara gaban shugaban jam’iyyar PDP na kasa
- Ana zargin wasu ‘yan majalisar NWC da yunkurin kawowa jam’iyyar hamayyar tasgaro a zaben 2023
Anambra - Akwai yiwuwar sabon rikici ya raba kan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP yayinda masu ruwa da tsaki a jihar Anambra suka alantar. Jaridar This Day ta bayyana wannan a wani rahoto.
Lamarin har ya kai wasu daga cikin shugabanni da masu ruwa da tsaki a PDP a jihar Anambra su na jifan wasu ‘yan majalisar gudanarwa na NWC na kasa da laifi.
‘Ya ‘yan PDP su na ganin ‘yan NWC sun shiryawa jamiyya zagon-kasa a babban zaben 2023.
Hakan na zuwa ne bayan uwar jam’iyya ta bada sharudan dawo da fam din shiga takara ga masu neman tikitin shugaban kasa a karkashin PDP a zabe mai zuwa.
A daidai wannan lokaci kuma, an ji labari cewa kwamitin yakin zaben Bukola Saraki ya yi kira ga jam’iyyar PDP ta ba kowa damar neman takarar shugaban kasa.
Earl Osaro Onaiwu ya na zargin sakataren jam’iyya, Samuel Anyanwu da mai bada shawara a kan harkokin shari’a, Kamaldeen Ajibade, SAN da kokarin baba-kere.
Osaro Onaiwu ya ce wadannan shugabanni biyu sun fara ne da zaben shugabanni na Anambra.
Shugaban PDP ya sa baki
A wani jawabi da ya fito daga bakin Emeka Nwankwo a madadin wasu ‘ya ‘yan PDP, an yi kira ga Dr. Iyorchia Ayu ya yi maza ya sa baki kafin abin ya yi kamari.
APC ta yi babban rashi yayin da masu biyayya ga ministocin Buhari suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar
Cif Emeka Nwankwo ya na barazanar cewa dinbin mutane za su sauya-sheka daga jam’iyyar PDP muddin ba ayi maza, an kammala zaben shugabanni a jihar ba.
Kafin yanzu, Peter Obi ya yi zama da shugaban PDP da ‘yan majalisarsa a kan matsalolin da ake zargin Chris Ubah da Linus Ukachukwu su na neman kawowa.
Babu kan ta a wasu jihohi
Haka zalika akwai irin wannan matsala a jihar Ekiti, inda wasu daga cikin magoya bayan Ayo Fayose suka sauya-sheka daga jam’iyyar hamayyar zuwa SDP.
Daily Trust ta ce a Legas kuwa, dattawan PDP ba su yi na'am da zaben shugabannin da Gwamna Douye Diri ya gudanar ba, ana zargin an yi son kai a wajen zaben.
Obasanjo ya ja kunnen jama'a
A makon jiya aka ji tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya nemi ‘yan Najeriya su raba kansu da zaben masu neman takarar da suke yi wa jama’a karya.
Olusegun Obasanjo ya yi kira ga al’umma su guji kada kuri’arsu ga duk wanda ke da'awar wasu ne su ka saya masa fam din takara saboda goyon bayansu da suke yi.
Asali: Legit.ng