Sanata Kwankwaso ya shiga Jam’iyyarsa ta 5 a tarihin siyasa bayan ya fice daga PDP
- Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi katin zama cikakken ‘dan jam’iyyar NNPP a garin Abuja
- Tsohon Ministan tsaron ya fice daga PDP ne kamar yadda ya yi shekaru kusan takwas da suka wuce
- A baya Kwankwaso ya yi takara a SDP, PDP, APC, kuma ya taba yin jam’iyyar SDP a lokacin soja
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana sabuwar jam’iyyar da ya shiga a sakamakon ficewa da ya yi daga PDP a ranar Talata.
‘Dan siyasar ya shiga jam’iyyar hamayya ta NNPP bayan tsawon makonni ana ta rade-radin cewa ya na shirin sauya-sheka daga PDP da ya dawo a shekarar 2018.
Saifullahi Hassan wanda yana cikin hadiman tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ya tabbatar da wannan labari a shafinsa na Twitter da karfe 4:47 na yamman yau.
Legit.ng Hausa ta fahimci Hon. Saifullahi Hassan ya wallafa hotunan Rabiu Kwankwaso a shafinsa yayin da yake karbar katinsa na zama cikakken ‘dan NNPP.
Sanata Kwankwaso ya karbi takardar shiga wannan jam’iyya ne daga hannun shugaban NNPP a mazabar Kwankwaso ta jihar Kano a babban birnin tarayya Abuja.
Katin NNPP ya shiga hannun Kwankwaso
“Labari da dumi-dumi: Mai girma Injiniya @KwankwasoRM ya karbi katinsa na zama ‘dan jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP)”
“...Daga hannun shugaban mazabarsa ta Kwankwaso a karamar hukumar Madobi, jihar Kano.” - Saifullahi Hassan
Za a ga wasu daga cikin jagororin NNPP na kasa irinsu Dr Boniface Aniebonam da kuma wasu mabiya Kwankwasiyya a lokacin da ake gabatar masa da katinsa.
NNPP za ta zabi shugabanni na kasa
Bayan nan kuma sai aka ji wani babban labarin cewa jam’iyyar NNPP za ta shirya zaben shugabanni na kasa a ranar Larabar nan, 30 ga watan Maris 2022.
Za a yi babban gangamin ne a filin folo na 1212 Polo Ground da ke unguwar Gwarinpa, Abuja
A wannan ranar ne jam’iyyar NNPP za ta zabi shugabanninta na kasa. A watan nan 'yan NNPP su ka gudanar da zaben shugabanni a kananan hukumomi da jihohi.
Tarihin siyasar Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa NNPP ce jam’iyya ta biyar da Kwankwaso zai shiga daga lokacin da ya shiga harkar siyasa shekaru talatin da suka wuce zuwa yau.
Injiniya Rabiu Kwankwaso ya ci zaben majalisa a 1992 ne a SDP. A karkashin PDP ya yi gwamna sau biyu. Sannan ya yi shekara hudu a APC tsakanin 2014 da 2018.
Kwankwaso ya shiga jam’iyyar DPN kafin a ruguza ta bayan mutuwar Janar Sani Abacha a 1998. Bayan an wargaza jam’iyyun siyasan ne sai aka kafa jam’iyyar PDP.
Injiniya Kwankwaso ya bar PDP
Dazu aka ji cewa sa’o’i 48 da jin labarin ficewar Abba Kabiru Yusuf daga PDP, sai Rabiu Kwankwaso ya bada sanarwar barin jam’iyyar hamayyar a takarda.
Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya sanar da shugaban PDP na mazabar Kwankwaso cewa ya raba jiha da jam’iyyarsu saboda wasu sabani da aka samu.
Asali: Legit.ng