Yanzu nan: Sanata Kwankwaso ya aikawa Jam’iyya takardar barin PDP, ya bayyana dalilansa

Yanzu nan: Sanata Kwankwaso ya aikawa Jam’iyya takardar barin PDP, ya bayyana dalilansa

  • A yau aka ji tsohon Gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya yi watsi da jam’iyyar PDP
  • Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga PDP a wasikar da ya aikawa shugaban mazaba
  • ‘Dan siyasar ya ce ya samu wasu sabani ne da suka gagara a iya shawo kansu da shi da jam’iyyar

Kano - A yau Talata, 29 ga watan Maris 2022, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar hamayya ta PDP.

Hakan ya na zuwa ne bayan an dauki dogon lokaci ana ta rade-radin cewa tsohon gwamnan na jihar Kano zai sauya-sheka daga jam’iyyar.

Wannan labari ya zo mana ne daga bakin Hadimin ‘dan siyasar, Saifullahi Hasan wanda ya fitar da takardar murabus din a dandalin Twitter.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya aikawa shugaban PDP na mazabarsa ta Kwankwaso a jihar Kano a ranar Talata, 29 ga watan Maris 2022.

Kara karanta wannan

Duk da Shugaban kasa ya sa baki, har yanzu APC na fama da rikicin cikin gida a jihohi

‘Dan siyasar ya ce ya datse duk wata alaka da ke tsakaninsa da jam’iyyar PDP a fadin kasar nan.

Kamar yadda aka gani a takardar, tsohon Ministan tsaron ya bayyana cewa yana mai takaicin sanar da jam’iyyar wannan mataki da ya dauka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso ya bar PDP Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Me ya yi zafi haka?

Da yake bayanin dalilinsa na barin PDP, tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ya ce an samu wasu matsaloli ne da aka gagara shawo kansu a jam’iyyar.

“A karshe na dauki matakin cewa ba zai yiwu in cigaba da zama a jam’iyyar PDP ba”
“Saboda haka na yanke cewa daga yau (Talata, 29 ga watan Maris 2022), na fita daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP.”

- Rabiu Musa Kwankwaso

Wannan takarda ta shiga hannun shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Kwankwaso a karamar hukumar Madobi, jihar Kano, har ya sa hannunsa.

Kara karanta wannan

Tun kafin a je ko ina, PDP ta samu kusan Naira miliyan 300 daga saida fam din takara

Sauya-shekar Kwankwaso a siyasa

Ba wannan ne karon farko da Kwankwaso ya bar PDP ba, ya yi haka a 2014 a lokacin ya na gwamna, ya sauya-sheka zuwa APC da ta karbi mulki.

A karkashin jam’iyyar PDP Sanata Kwankwaso ya zama Gwamna sau biyu a jihar Kano, kuma gwamnatin PDP ta nada shi Ministan tsaro na kasa a 2003.

Lokacin da kafar Kwankwaso ta tsallaka

A wata hira da aka yi da Rabiu Musa Kwankwaso kwanakin baya, an ji ya soki salon tafiyar jam’iyyarsa ta PDP da APC da ya bari kafin zaben 2019.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya na ganin babu abin da APC da PDP za su yi alfahari da shi a 2023, don haka ya nemi mutane su nemi wata mafitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng