Masu neman mulkin Najeriya a PDP sun karu, Gwamnan Ribas ya shirya gwabzawa
- Gwamna Nyesom Wike ya ce da shi za a nemi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP
- Nyesom Wike ya ayyana burinsa na neman mulkin Najeriya ne a lokacin da ya ziyarci Benuwai
- A cewar Wike, lokacin da wasu ‘yan siyasa suke sauya-sheka daga PDP, shi ne ya zauna a jam’iyyar
Benue – Mai girma Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana shirinsa na neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Jaridar The Cable ta ce Gwamnan na jihar ribas ya bayyana wannan ne a lokacin da ya ziyarci ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Benuwai a ranar Lahadin nan.
Nyesom Wike ya bayyana cewa yana sa ran jam’iyyar adawa ta PDP za tayi galaba a zabe mai zuwa.
“Idan za ka yi takara, ba a bagas za a mika maka mulki, karba ake yi. Na fito kuma zan karbe mulki daga hannun APC, in mikawa PDP da yardar Ubangiji.”
“Ubangiji ya bamu duk abin da ake bukata. Shiyasa Ubangiji ya sa APC take tafka kuskure a duk rana, ta haka za ka gane cewa Ubangiji yana tare da kai.”
Da yake jawabi kamar yadda Vanguard ta kawo rahoto, gwamnan ya ce ya zabi ya ayyana niyyarsa a Benuwai ne saboda irin alakar da ke tsakaninsa da jihar.
Alakar Wike da 'Yan Benuwai
“Bari in godewa mutanen Benuwai da suka karbe ni domin in yi masu magana. Na bayyana shirin takara a karon farko a Benuwai ne saboda alaka ta da su.”
“A yau ba za ka iya yin maganar zaman lafiya a kasar nan ba, kuma dole a fahimci cewa ba zai yiwu ayi mulki ba tare da an samar da zaman lafiya ba.”
“Abin da ake fara fadawa wanda aka rantsar a mulki shi ne zai tsare lafiya da dukiyoyin mutane, idan ba za ka iya yin wannan ba, babu batun jagoranci.”
Wike ya soki gwamnatin APC
A halin da ake ciki, Wike ya ce masu hannun jari ba za su zuba kudinsu a Najeriya ba saboda rashin tsaro da rashin bin doka domin ana yi wa kotu taurin-kai.
A cewarsa, masu neman mulki a PDP a yau, su ne wadanda suka tsere daga jam’iyya a baya, har ya kira su (bai ambaci suna ba) da zama matsalar PDP a zaben 2015.
Zaben APC na kasa
Ku na da labari cewa an fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a matakin APC na kasa, kuma babu wasu daga cikin ‘Yan takarar shugaba Muhammadu Buhari.
Abubakar Kyari ne ya zama mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa, a yankin Kudu kuwa aka zabi Emma Eneukwu a maimakon Farouk Adamu Aliyu da Ken Nnamani.
Asali: Legit.ng