An kai wa Buhari kukan wasu Gwamnoni 2, an nemi ya ja masu kunne da kyau kafin 2023
- Kungiyar Nigeria Union of Local Government Employees ta kebe wasu gwamnoni biyu, ta yi tir da su
- Wannan kungiya ta ma’aikatan kananan hukumomi ta ce gwamnonin na adawa da su samu ‘yanci
- Kayode Fayemi da Rotimi Akeredolu na Ekiti a Ondo ake zargin su na yakar kananan hukumomi
Abuja - Kungiyar Nigeria Union of Local Government Employees wanda aka fi sani da NULGE ta na zargin wasu gwamnonin kasar nan da kawo mata cikas.
Rahoton da muka samu daga Daily Trust ya nuna cewa kungiyar NULGE ta ma’aikatan kananan hukumomi ta na zargin gwamnonin da neman murkushe su.
NULGE ta ce Kayode John Fayemi da Rotimi Akeredolu za su yi wannan ne ta hanyar hana a amince da kudirin da zai ba kananan hukumomi cin gashin kai.
Hakan ta sa kungiyar tayi wani taro na musamman, inda a karshe tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja-kunnen gwamnonin na jam’iyyarsa.
Shugaban NULGE na kasa, Ambali Olatunji ya shaidawa manema labarai cewa abin da gwamnonin ke yi zai iya kawowa APC matsala a zabe mai zuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Za ayi ta fama da matsalar tsaro - Olatunji
Ambali Olatunji ya ce kokarin da wasu gwamnoni ke yi na hana kananan hukumomi samun ‘yanci shi ne zai kara jawo matsalar ‘yan bindiga da sauran ta’adodi.
A ra’ayin shugaban kungiyar, kashe kananan hukumomi ne babban abin da ya jawo ake fama da rashin tsaro, da kiran a raba Najeriya da dai laifuffuka iri-iri a yau.
NULGE ta yabi Gwamnoni 2 a kasar nan
An rahoto Olatunji yana cewa babu kishin kasa da kaunar jama’a a matsayar da wadannan gwamnoni da ke mulki a kudu maso yammacin Najeriya suka dauka.
A jawabin da ya gabatar a gaban ‘yan jarida, shugaban NULGE ya yabawa Nyesom Wike na jihar Ribas da takawaransa, Mai girma Abubakar Badaru na jihar Jigawa.
Nigeria Union of Local Government Employees ta ce gwamnonin biyu sun fita zakka domin sun fito fili, su na goyon bayan a ba kananan hukumomi cin gashin kai.
‘Yan majalisa sun yi wa tsarin mulkin garambawul domin kananan hukumomi su samu ‘yancin kansu ba tare da dogara da gwamnoni ba, abin da wasu ke yaki da shi.
An kawo sabuwar doka a zaben APC
An ji cewa duk wani Minista ko wanda yake rike da kujerar da Shugaban kasa ko wani mai mulki ya ba shi, bai da ta-cewa a zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa.
Sabuwar sanarwar da aka fitar dazu ta tabbatar da cewa masu mukamai a gwamnati sai dai su halarci gangamin APC a matsayin ‘yan kallo, ba masu yin zaben ba.
Asali: Legit.ng