Atiku, Ribadu, Tambuwal, da wadanda suka yafe neman Shugaban kasa, su ka nemi Gwamna
- An yi wasu ‘yan siyasa da suka dauko ta da zafi a siyasar Najeriya, daga baya suka bari ya huce
- Akwai wadanda a tashin farko suka nemi kujerar shugaban kasa, sai su ka koma takarar gwamna
- Zama shugaba a kasa irin Najeriya yana da matukar wahalar gaske, abin sai wanda yake da rabo
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta bi tarihi, ta kawo sunayen irin wadannan ‘yan siyasa da suka fara da babban buri, amma dole suka hakura daga bisani:
1. Atiku Abubakar
Na farko a wannan jerin shi ne Alhaji Atiku Abubakar wanda ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 1993, amma ya rasa tikitin SDP a wajen Marigayi MKO Abiola.
Daga baya Atiku ya hakura da shugaban kasa, ya yi takarar gwamna, kuma ya yi nasara a 1999. Duk da ya ci zabe, bai yi gwamna ba, ya zama mataimakin shugaban kasa
2. Nuhu Ribadu
Shi kuma Mallam Nuhu Ribadu ya shiga siyasa ne da neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar AC. Sai dai tsohon shugaban na EFCC bai yi nasara a 2011 ba.
Bayan kusan shekaru uku sai Ribadu ya nemi kujerar gwamnan jihar Adamawa a PDP. A nan ma dai bai dace ba, daga baya ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
3. Aminu Waziri Tambuwal
Da farko Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya nemi ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2015, a lokacin shi ne shugaban majalisar wakilan tarayya na kasa.
Idan za a tuna, Aminu Tambuwal ya hakura da wannan buri a APC, ya zama gwamna a jihar Sokoto. Kusan wannan abin ya maimaita kansa a PDP a zaben 2019.
4. Datti Baba Ahmed
Dr. Datti Baba Ahmed yana cikin wadanda suka nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a 2018, amma sam bai kama hanyar nasara ba.
Da aka dawo 2022 sai aka ji ‘dan siyasar ya na so ya yi takarar gwamna a jihar Kaduna. Dr. Baba Ahmed zai gwabza da APC mai mulki idan PDP ta ba shi tuta.
5. Rochas Okorocha
Sanata Rochas Okorocha ya taba neman ANPP ta tsaida shi a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a 2003, amma bai yi nasara ba. Daga nan sai aka ji ya koma PDP.
Okorocha ya kafa jam’iyyar AA da niyyar zama ‘dan takarar shugaban kasa a 2007, shi ma hakan bai yiwu ba. A karshe dai ya lashe zaben gwamnan Imo a zaben 2011.
Matsayin Yarbawa a 2023
A jiya aka ji cewa ba dole ba ne mulki ya fada hannun su Asiwaju Bola Tinubu ko Yemi Osinbajo domin ba a tsaida wata yarjejeniya da Yarbawa a jam’iyyar APC ba
Akwai masu ganin kafin a kafa APC shekaru goma da suka wuce, sai da aka yi yarjejeniyar bayan Muhammadu Buhari, shugabanci zai koma kasar Yarbawa a 2023.
Asali: Legit.ng