Yadda mutane kusan 200 za su goge raini wajen neman mukamai 22 a Jam’iyyar APC

Yadda mutane kusan 200 za su goge raini wajen neman mukamai 22 a Jam’iyyar APC

  • Jam’iyyar APC na shirin gudanar da zaben shugabannin da za su rike mukamai a majalisar NWC
  • Akwai ‘yan takara sama da 160 da suka saye fam, su na neman kujeru a matakin jam’iyyar na kasa
  • Zuwa yanzu, jam'iyyar ta tara makudan miliyoyin kudi daga ‘yan siyasan da suke harin mukaman

Abuja - Akalla mutane 169 aka tabbatar da cewa sun saye fam domin neman takarar mukamai dabam-dabam a majalisar NWC ta jam’iyyar APC.

Premium Times ta fitar da wani rahoto na musamman a ranar Laraba, 23 ga watan Maris 2022 da ya nuna mutane kusan 170 za su nemi mukamai 22.

Mutane bakwai su ka saye fam domin neman shiga takarar shugaban jam’iyyar APC na kasa. Akwai Tanko Al-Makura da kuma Abdullahi Adamu.

Sai kuma George Akume, Sani Musa, Saliu Mustapha da Mohammed Etsu. Akwai Abdulaziz Yari wanda shi kadai ne bare daga Arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

Mataimakin shugaban jam'iyya

‘Yan takara shida ne suke neman kujerar babban mataimakin shugaban jam’iyya na kasa. Isa Yuguda; Yakubu Dogara da Abubakar Girei su na cikinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran masu neman wannan kujera su ne; Sunny Moniedafe, Abubakar Kyari da Faruk Adamu Aliyu wanda ake zargin yana tare da fadar shugaban kasa.

A masu neman irin wannan kujera a yankin kudu akwai Ken Nnamani da Emmanuel Joseph.

Jam’iyyar APC
Ana tantance masu neman takara a APC Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sakataren APC na kasa

Zuwa yanzu, ‘yan takara hudu suka saye fam na neman zama sakataren APC na kasa; Iyiola Omisore, Adebayo Shittu; Olaiya Olaitan, da Ife Oyedele.

Rahoton ya ce Victor Giadom da Yekini Nabena su na neman karin matsayi a NWC. Za su yi takarar mataimakin shugaban jam’iyya na kudu maso kudu.

Shugaban matasa da wasu kujerun

Dada Olusegun, Dayo Israel, Kareemat Abiola, Olalekan Edwards da Buhari Sadeeq duk sun ci burin zama shugaban matasa na jam’iyyar APC na kasa.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa

Dayo Israel yana tare da bangaren Tinubu yayin da aka ji Sahabi Yusuf daga Arewa maso yamma ya koma neman kujerar mataimakin shugaban matasa.

Ismaeel Ahmed yana harin kujerar sakataren gudanarwa na kasa. Effiom Boco, Mary Ekpere da Betta Edu duk sun saye fam na shugaban matan jam’iyya.

Ya labarin takarar Abdullahi Adamu?

An ji labari cewa zai yi wahala kusoshin APC da Gwamnonin jihohin Kudancin Najeriya su zabi wanda Shugaban kasa yake so a zaben shugabannin da za ayi.

Wani babba a jam’iyyar APC ya ce Abdullahi Adamu bai kaunar tsarin karba-karba, kuma yana sukar masu goyon bayan hakan, don haka ba za su zabe shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng