‘Yan Majalisa 15 sun hadu, za a sayawa Gwamnan PDP fam domin ya zarce a kan mulki
- Hon. Ahmadu Umaru Fintiri ya samu karfin gwiwar sake neman takarar gwamna a jihar Adamawa
- Wasu ‘yan PDP a majalisar dokokin Adamawa sun ce za su sayawa Gwamnan fam domin ya koma ofis
- Rt. Hon. Aminu Iya Abbas da sauran ‘yan majalisar dokoki sun ce Ahmadu Fintiri ya dace ya yi tazarce
Adamawa - Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Adamawa, sun sha alwashin cewa za su sayawa Ahmadu Umaru Fintiri fam na takarar gwamna.
Jaridar Daily Trust ta ce ‘ ya 'yan PDP a majalisar dokokin ne suka yi wannan alkawari da nufin ganin Ahmadu Umaru Fintiri ya koma kan kujerar da yake kai.
Jam’iyyar PDP mai rinjaye ta na da kujeru 14 a majalisar jihar Adamawa, APC ta na kujeru 11.
Shugaban majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Aminu Iya Abbas ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa Umaru Fintiri ya dace ya zarce kan karagar mulki.
A cewar Hon. Aminu Iya Abbas, ayyukan da gwamnan ya yi sun sa ya cancanta da ya koma ofis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Saboda yadda da muka yi da Mai girma gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, mu ‘Yan PDP a majalisa, mun dauki matakin saya masa fam din nuna sha’awa da na shiga takara.”
- Rt. Hon. Aminu Iya Abbas
Akwai mai adawa da Gwamna?
The Nation ta ce har zuwa yanzu babu wani ‘dan jam’iyyar PDP mai mulki da ya nuna yana sha’awar namen takarar kujerar gwamna a jihar Adamawa.
Hakan ya kara tabbatar da cewa gwamnan zai nemi ya koma kujerarsa domin kammala wa’adin karshe, watakila ba tare da ya samu hamayya a cikin gida ba.
A yayin da Aminu Iya Abbas yake bada wannan sanarwa a gaban majalisar dokokin Adamawa da ke babban birnin Yola, akwai wasu ‘ya ‘yan PDP a gefensa.
Abbas da sauran abokan aikinsa za su biya Naira miliyan 21 da ake bukata domin sayen fam din shiga zaben fitar da gwani na kujerar gwamna a jam’iyyar PDP.
Shugaban majalisar ya ce wannan abin da za su iya bai nufin majalisa ba su cin gashin kansu. Abbas ya ce su na yin duk aikin da ya dace bisa tsarin mulki.
'Yan majalisa na cikin hadari
Kun ji cewa babu mamaki kotu ta tsige wasu 'yan majalisar dokokin jihar Imo a sakamakon sauya sheka da suka yi daga jam'iyyar da ta ba su nasara a 2019.
‘Yan Majalisar da suka shiga dar-dar su ne: Collins Chiji, Amarachi Iwuanyanwu. Uju Onwudiwe, Ngozie Obiefule, Johnson Duru, Arthur Egwim, da wasu su 17.
Asali: Legit.ng