Zaben shugabanni: Gwamnonin Yarbawan APC sun yi watsi da ‘Dan gani-kashenin Buhari

Zaben shugabanni: Gwamnonin Yarbawan APC sun yi watsi da ‘Dan gani-kashenin Buhari

  • Gwamnonin kudu maso yammacin kasar nan da ke mulki a APC su na tare da Duerimini Isaacs Kekemeke
  • Rotimi Akeredolu ya ce Hon. Duerimini Kekemeke shi ne ‘dan takararsu na mataimakin shugaban jam'iyya
  • A game da kujerar Sakatare na kasa, ana tunanin gwamnonin jam’iyyar ta APC ba su goyon-bayan Ife Oyedele

Ondo - Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya sun fitar da matsaya a kan zaben shugabanni da za ayi.

Legit.ng ta fahimci cewa gwamnonin yankin sun bayyana goyon bayansu ga Hon. Duerimini Isaacs Kekemeke a matsayin ‘dan takararsu na shugaban jam’iyya.

Duerimini Isaacs Kekemeke ne gwamnonin za su marawa baya a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin kudu maso yamma.

Gwamnonin APC sun bayyana wannan ne a wani jawabi da suka fitar ta bakin kwamishinan yada labarai da wayar da kan al’umma na Ondo, Mista Donald Ojogo.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi kutun-kutun, aka tunbuke Sakataren APC kafin Mala Buni ya dawo daga Dubai

Donald Ojogo ya ce Duerimini Isaacs Kekemeke ya samu yardar Mai girma gwamna Oluwarotimi Akeredolu SAN da sauran gwamnonin APC na bangaren da ya fito.

Hon. D. Isaac Kekemeke
Zaben shugabanni: Gwamnan Ondo tare da Hon. Kekemeke Hoto: Tola Asaolu
Asali: UGC

Dalilin mu na goyon bayan Kekemeke

A jawabin da Ojogo ya fitar, an ji yana cewa Duerimini Isaacs Kekemeke ya cancanci ya rike wannan mukami, kuma zai taimakawa kudu maso yamma a jam’iyya.

Ojogo ya yi karin haske da cewa kujerar mataimakin shugaban jam’iyya Kekemeke zai nema ba sakatare ba, sannan ya ja kunnen masu neman kawo masu rikici a APC.

Kwamishinan ya shaidawa manema labarai cewa an ware wannan kujera ta fito daga jihar Ondo. Sannan kuma sakataren APC na kasa zai fito daga shiyyar Oyo/Osun.

Oyedele zai kai labari?

Rahoton ya bayyana cewa wadannan gwamnoni ba su goyon bayan shugaban kamfanin Niger Delta Power Holding, Ife Oyedele ya zama sakataren jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin APC

Oyedele shi ne ‘dan takarar Bola Tinubu, kuma ana tunanin Muhammadu Buhari na goyon bayansa.

Oyedele mutumin jihar Ondo kuma ya dade yana tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a siyasa. Tun a zamanin jam’iyyar CPC, Oyedele yake tafiya da Buhari.

A zabi mai jini - Tambuwal

Kwanaki Gwamnan Sokoto, Rt. Aminu Tambuwal ya yi wa kungiyar dalibai huduba, ya hure masu kunne a kan zaben wanda ya tsufa domin ya zama shugaban Najeriya.

Rt. Hon. Aminu Tambuwal ya fadawa shugabannin NANS cewa duk wanda ya zarce shekara 60 a Duniya, yana shirin haduwa da Ubangijinsa ne, ba jiran ya mulki kasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng