Gwamna Aminu Tambuwal ya ba matasa satar amsar wanda za su marawa baya a 2023

Gwamna Aminu Tambuwal ya ba matasa satar amsar wanda za su marawa baya a 2023

  • Gwamnan jihar Sokoto ya ce kul ‘Yan Najeriya su ka dauko tsoho a matsayin wanda zai jagorance su
  • Aminu Waziri Tambuwal ya ba ‘yan kungiyar NANS shawarar su zabi wanda bai wuce shekara 60 ba
  • Manyan masu harin shugaban kasa irinsu Atiku Abubakar da Bola Tinubu duk sun zarce wannan shekaru

Jigawa - Mai girma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ba matasan kasar nan shawarar su guji zaben tsoho ya zama shugaban kasa a 2023.

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi wannan kira ne a lokacin da ya hada da kungiyar daliban jami’an kasar nan. Premium Times ta kawo wannan rahoton.

Aminu Waziri Tambuwal ya hadu da shugabannin kungiyar NANS na duka reshen jihohin Arewacin Najeriya a jihar Jigawa, inda su ka yi masa mubaya’a.

Kara karanta wannan

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa saboda sha'awar kujerar gwamna

Kwamishinan matasa da harkokin wasanni na jihar Sokoto, Bashir Usman ne ya wakilci Aminu Waziri Tambuwal a wajen wannan ganawa da ‘yan kungiyoyin.

A madadin Gwamna Aminu Tambuwal mai shekara 56, Bashir Usman ya fadawa daliban cewa a matsayinsu na masu kasar nan, bai dace su ba tsoho kuri’arsu ba.

Aminu Tambuwal
Gwamnan Sokoto Tambuwal Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Kwamishinan Sokoto

“Matasan Najeriya ku ne masu kasar nan, duk wanda ya zarce shekara 60 a Duniya, yana shirin haduwa da Ubangijinsa ne – ba jiran ya mulki kasa ba.”
Mu na bukatar shugaban kasa mai lafiya, wanda zai iya zagaye a fadin kasar nan a rana guda domin samun bayanai a kan abubuwan da ke damun al’umma.”
“Ba shugaban kasar da zai zauna yana hutawa a ofishinsa ba, yana jiran bayanan da mutanensa suka tace, kafin su kawo masa.” – Aminu Tambuwal.

Kara karanta wannan

Babu shiri, dole Shugaban PDP ya tada taro saboda za a kawo tashin hankali kan tutar 2023

A guji dauko maras lafiya

Haka zalika gwamnan ya bukaci ‘Yan Najeriya su kauracewa zaben wanda bai da cikakken lafiya ko yake fama da larurar tsufa a matsayin shugaban kasa a 2023.

Kafin a tashi a wannan zama, Platinum Post ta ce Rt. Hon. Tambuwal ya yi magana game da yajin-aikin ASUU, ya ce rufe jami’o’in kasar da aka yi abin takaici ne.

Rikici a PDP?

Ku na sane da cewa an yi wani zama na musamman da Gwamnonin PDP, Walid Jibrin; Atiku Abubakar; Ike Ekweremadu; da Bukola Saraki su ka halarta a Abuja

An samu sabani a taron jam’iyyar PDP bayan wani Gwamnan kudu ya kawo shawarar da za tayi waje da Atiku, Saraki da su Tambuwal daga takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng