A karshe, Osinbajo ya zauna da Buhari a kan shirin takarar shugaban kasa a zaben 2023

A karshe, Osinbajo ya zauna da Buhari a kan shirin takarar shugaban kasa a zaben 2023

  • Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya dauki mataki a game da takara a zaben 2023
  • Ana kyautata zaton Yemi Osinbajo ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari shirin takararsa
  • Shugaban kasar ya nunawa Osinbajo ya jarraba sa’arsa, amma babu tabbacin zai mara masa baya

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya sanar da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari shirinsa na neman takarar shugaban Najeriya.

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa bayan wata da watanni ana rade-radi, Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa ya na sha’awar shugabancin kasa.

Farfesa Yemi Osinbajo ya fadawa mai gidansa cewa idan so samu ne, ya karbi ragamar shugabancin kasar nan daga hannunsa a Mayun 2023.

Osinbajo yana ganin hakan zai bada damar cigaba da samun nasarorin da aka gani daga lokacin da gwamnatin APC ta karbi mulki a hannun jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Za a kafa bangarorin siyasa na musamman a duk reshen cocin da Osinbajo yake aikin Fasto

Jaridar Daily Trust ta ce har zuwa yau, mataimakin shugaban kasar Najeriyar bai sanar da Duniya game da burinsa na tsayawa takara a zabe mai zuwa ba.

Shugaba Buhari da Mataimakinsa
Buhari da Farfesa Osinbajo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda ta kasance a Aso Villa

“Shakka babu, mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya fadawa shugaban kasa cewa yana so ya gaje shi.”
“Mataimakin shugaban kasar ya fara tuntubar wasu manyan kasa, wadanda su ka ba shi kwarin gwiwa, su ka karfafa masa baya ya nemi mulki.”
“Daga nan su ka ba shi shawarar ya fadawa shugaban kasa da kan shi. Sun fada masa cewa ka da ya bari wasu su fadawa Buharin a madadinsa.”

- Majiya

Wata majiyar ta shaidawa jaridar cewa da Osinbajo ya kai wa Buhari maganar, kamar yadda ya saba, sai ya yi murmushi kurum yana sauraron abin da ya ke fada.

Kara karanta wannan

Sawun giwa: Magoya bayan Tinubu sun fadawa su Osinbajo su hakura da takara a 2023

Buhari ya yi masa irin na Tinubu

“Shugaba Buhari ya nunawa Osinbajo cewa zai iya jarraba sa’arsa, amma bai tabbatar masa da cewa zai mara masa baya a kan sauran ‘yan takara ba.”
Haka shugaban kasar ya yi a lokacin da Bola Tinubu ya zauna da shi a fadar Aso Villa, bai nuna masa ya janye takara ba, bai kuma ce yana tare da shi ba.

- Wata majiyar

Wa zai samu tikitin APC a 2023

Idan dai ta tabbata, Osinbajo zai gamu da babban kalubale domin tsohon ubangidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya na cikin wadanda za su nemi takara.

Ana tunanin cewa wajen neman tikitin jam’iyyar APC, Osinbajo zai gwabza da Ministoci irinsu Rotimi Amaechi da Chris Ngige da Gwamna Kayode Fatemi.

A cikin wadanda su ke neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC akwai Sanata Rochas Okorocha da Sanata Orji Uzor Kalu da gwamna Dave Umahi.

Kara karanta wannan

Tafiyar Buhari Landan: Har yanzu shuru, Buhari bai sanar da Majalisa ya mika mulki ga Osinbajo ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng