Zaben 2023: Idan na shiga Aso Villa, kowane yaro zai yi karatu kyauta inji Sanatan APC

Zaben 2023: Idan na shiga Aso Villa, kowane yaro zai yi karatu kyauta inji Sanatan APC

  • Rochas Okorocha ya bayyana shirin da yake da shi idan shugabancin Najeriya ya fado hannunsa
  • ‘Dan siyasar ya ce akasarin ‘yan Najeriya sun yi imani da shi saboda zai kawo hadin-kai a kasar nan
  • Sanata Okorocha ya ce zai yi bakin kokarinsa wajen ganin kowane yaro ya je makaranta a mulkinsa

Abuja - Sanatan Imo ta yamma a majalisar dattawa, Rochas Okorocha ya bayyana cewa idan ya samu dama a zaben 2023, zai karfafa hadin-kan al’umma.

Sanata Rochas Okorocha ya bayyana wannan a lokacin da aka yi wata hira ta musamman da shi a shirin Political Paradigm a gidan talabijin Channels TV.

“Mafi yawan ‘yan Najeriya sun yarda da ni saboda abubuwan da na fada – daga hadin-kan kasar nan; zan iya kawo zaman lafiya, kuma an amince da ni.”

Kara karanta wannan

Sanusi II: Abu 1 da ya sa Jonathan da Ganduje suka tsige ni daga CBN da sarautar Kano

“Sun yarda da Rochas da ya ce zai kawo zaman lafiya idan ya zama shugaban kasa, zai yi wannan ne saboda irin abubuwan da na yi a baya a kasar nan.”
“Ba na nuna wariyar kabila ko addini, abin da yake gaba na kurum shi ne Najeriya.” – Okorocha.

Okorocha ya kara da cewa babban abin da ya sa yake neman shugabanci shi ne jama’a su na bukatar shugaban da ya damu da su, sannan ya gyara kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatan Imo
Sanata Rochas Okorocha Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Ina da tausayin talaka - Okorocha

Rahoton ya ce tsohon gwamnan yana ganin ya sha ban-bam da sauran masu neman mulki saboda irin yadda yake kaunar talaka kamar yadda aka gani.

Okorocha ya ce ya nuna yadda ya damu da rayuwar al’umma – musamman masu karamin karfi, talakawa da zaurawa a gidauniyarsa ta Rochas Foundation.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Kowa zai je makaranta a kyauta

Idan ya zama shugaban kasa, Okorocha ya ce za a ga wasu daga cikin abubuwan da ya yi a Imo, daga ciki shi ne kowane yaron kasar nan ya yi karatu kyauta.

Ganin akwai yara miliyan 14.5 da ba su zuwa makaranta a yau, Okorocha ya ce zai sadaukar da rayuwarsa domin ya tabbatar kowa ya yi karatu kamar ‘dansa.

‘Dan siyasar ya ce baya ga haka, gwamnatinsa za ta dage wajen ganin matasa sun daina zaman banza.

Atiku zai yi takara?

A jiya ne Atiku Abubakar ya tabbatarwa kowa cewa zai nemi takarar shugaban kasa a 2023, ya ce mutanen kasar nan su na matukar bukatar PDP ta dawo mulki.

Atiku Abubakar yana ganin a yau ana bukatar shugaban da ya san kan aiki, kuma jagoran da zai iya hada-kan al’umma, ya ce za a samu duk wannan a wurinsa.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Yadda Gwamnatin Jonathan ta so bankara doka domin hana Buhari mulki

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng