Abin da PDP za tayi kafin tayi nasara a zabe - Gwamna Tambuwal ya bada lakanin 2023

Abin da PDP za tayi kafin tayi nasara a zabe - Gwamna Tambuwal ya bada lakanin 2023

  • Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya na ganin jam’iyyar PDP za ta iya komawa kan mulki a 2023
  • Dabarar kuwa ita ce a wayar da kan mutane, sannan a nemo kuri’un mutanen da ke zama a karkara
  • Kafin PDP ta iya doke APC a 2023, Gwamnan na jihar Sokoto yana ganin sai an yi zabe na adalci

Sokoto - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya nuna cewa akwai abubuwan da jam’iyyar PDP ta ke bukatar yi kafin ta doke APC a zaben 2023.

Jaridar Tribune ta rahoto Aminu Waziri Tambuwal yayi wannan bayani bayan sakamakon zabukan da aka gudanar a Abuja, Imo, Ondo, Filato da sauransu.

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya fitar da jawabi ta bakin hadiminsa, Muhammad Bello, yana cewa PDP ta na bukatar ta wayar da kan masu kada kuri’u a zabe.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Mai taimakawa gwamnan wajen yada labarai da hulda da ‘yan jarida, ya ce akwai bukatar jam’iyyar adawar ta tsaya tsayin daka domin yakar magudin zabe.

Haka zalika Waziri Tambuwal ya bada shawara ga PDP cewa ta maida hankali wajen tattaro kuri’un mutanen karkara idan har suna son ganin sun doke APC.

Tambuwal 2019
Kusoshin PDP a Sokoto a 2019 Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Post ta ce gwamnan ya yi wannan bayani ne a lokacin da ‘yan kwamitin yakin neman takarar Bukola Saraki suka kawo masa wata ziyara ta musamman.

Da yake jawabi a Sokoto a ranar Litinin, Aminu Tambuwal ya ce kan ‘yan jam’iyyar PDP a hada yake domin ganin sun karbe shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa.

Kira ga Gwamnatin Buhari

Gwamnan ya yi kira ga Muhammadu Buhari ya yi kokarin wajen ganin an yi zaben adalci a 2023, ya ce shugaban kasar ya ci moriyar zaben kwarai a shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Duka Gwamnonin APC za su yi zaman musamman domin dinke sabuwar baraka kan mukamai

A cewar Tambuwal, al’umma sun yi wa shugaban Najeriyar adalci domin kuwa sun yafe masa laifinsa na yin juyin mulki a 1984, suka zabe shi a mulkin farar hula.

“Najeriya ta na bin shi bashi, a yanzu dole ya kare dukiya da rayukan al’umma, sannan ya shirya zaben gaskiya.” - Aminu Tambuwal.

Daga cikin shawarar da Tambuwal ya ba PDP shi ne ta lura da zabukan da aka yi kwanan nan, ta dauki darasi. Gwamnan ya ce su na da abin da ake nema, ayi nasara.

Gwamnatin Oyo v EFCC

Kwanan nan aka ji Jami’an EFCC sun tsare babban Akawun jihar Oyo, Gafar Bello, a game da bacewar wasu Naira biliyan 9 daga asusun kananan hukumomin jihar.

Gwamnatin jihar Oyo ta shigar da kara gaban Alkali mai shari’a U. N. Agomoh na kotun tarayya da ke Ibadan, tana cewa hukumar EFCC ta matsawa jami’an jihar lamba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe zaben maye gurbi na majalisun tarayya a jihohi biyu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng