Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya tsokano fushin Jami’an DSS da kalaman da ya yi

Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya tsokano fushin Jami’an DSS da kalaman da ya yi

  • Shugaban jam’iyyar PDP, Dr. Iyorchia Ayu ya na zargin DSS da yi wa 'yan jam'iyyar adawa barazana
  • Hukumar DSS ta musanya wannan zargi na Iyorchia Ayu, ta ce ba a san ta da wannan aika-aikan ba
  • Peter Afunanya ya fitar da jawabi yana mai raddi, ya ce burinsu shi ne tsare al’ummar Najeriya kurum

FCT, Abuja - A ranar Litinin, 28 ga watan Fubrairu 2022, hukumar DSS ta kasa tayi kaca-kaca da shugaban jam’iyyar PDP na kasa watau Dr. Iyorchia Ayu.

Daily Trust ta ce jami’an tsaron masu fararen kaya sun dura kan Iyorchia Ayu ne a sakamakon kalaman da aka ji yana furtawa a game da aikin hukumar.

An rahoto Iyorchia Ayu yana mai cewa jami’an DSS sun kware wajen yi wa ‘Yan Najeriyan da ba su aikata laifin komai ba da kuma ‘yan hamayya barazana.

Kara karanta wannan

Da sake: PDP ba ta yarda ba, za ta je kotu kan tunbuke Mataimakin Gwamnan Zamfara

Mai magana da yawun hukumar tsaron na kasa, Peter Afunanya ya fitar da jawabi na musamman, ya na mai yi wa shugaban jam’iyyar adawan raddi.

A jawabin da ya fitar a garin Abuja, Peter Afunanya ya ce sam babu adalci a kalaman na Dr. Ayu. A cewar Afunanya DSS na kokarin gujewa shiga harkar siyasa.

Jami’an DSS
Jami'an tsaro a bakin aiki Hoto: www.currentschoolnews.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin Peter Afunanya

“Hankalin DSS ya je ga wasu kalamai da ba su dace ba da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu ya yi a kan jami’an tsaro har da DSS.”
“Duk da cewa hukumar ta na gujewa tsoma kanta cikin harkoki musamman wanda ya shafi ‘yan siyasa, ta na bukatar nesanta kanta daga kalamansa.”
“DSS ta na ganin babu adalci, ba gaskiya ba ne, babu tabbas, kuma kalaman na sa abin dariya ne.”

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da kakakin PDP ya rasu awanni bayan shagalin cika shekaru 50

“La’akari da ya yi aiki a matsayin shugaban majalisar dattawa, Ministan ilmi, na harkokin cikin gida da na muhalli, ya san DSS ba ta barazana ga kowa.”
“Idan har kuma ya taba amfani da dakarun DSS da aka ba shi a wancan lokaci wajen yin aikin assha ba tare da an sani ba, to yanzu abubuwa sun canza.”

-Peter Afunanya

Vanguard ta rahoto jami'in ya ce Ayu ya san DSS ta na bin doka, kuma manufar ta ita ce kare al’umma, kuma za ta cigaba da yin hakan, kuma ba za ta kare mai laifi ba.

Tsige gwamnan Zamfara

Ku na da masaniya cewa mai magana da yawun bakin PDP na kasa, Debo Ologunagba ya ce za su nemi su kare Alhaji Mahadi Aliyu Gusau a kotu kan tsige shi da aka yi.

Debo Ologunagba da PDP su na ganin ‘Yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun saba doka wajen tunbuke Mahadi Gusau daga kujerarsa, don haka za su je gaban Alkali.

Kara karanta wannan

Duka Gwamnonin APC za su yi zaman musamman domin dinke sabuwar baraka kan mukamai

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng