Da sake: PDP ba ta yarda ba, za ta je kotu kan tunbuke Mataimakin Gwamnan Zamfara
- Jam’iyyar PDP tana da ja a kan tunbuke Alhaji Mahadi Aliyu Gusau da aka yi daga kan kujerarsa
- Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Debo Ologunagba ya bayyana matsayar jam’iyyar adawa
- Ologunagba ya nuna cewa za su kai kara kotu domin majalisar dokokin Zamfara ba ta bi doka ba
Abuja - Jam’iyyar PDP ta ce ta na kokarin ganin ta kalubalanci tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Mahadi Aliyu Gusau da aka yi daga ofis.
Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar. PDP ta wallafa matsayar da ta ke kai a shafin Facebook.
Debo Ologunagba ya shaidawa Duniya cewa majalisar dokokin jihar Zamfara ta saba doka wajen tsige Mahadi Aliyu Gusau, don haka cire shi bai halatta ba.
Jam’iyyar hamayyar ta ce tana duba abin da ya faru domin daukar matakin da ya dace da dokar kasa.
A ranar Lahadin da ta wuce, 27 ga watan Fubrairu 2022, jaridar Vanguard ta rahoto kakakin jam’iyyar PDP na kasa, yana bayanin matakin da za su dauka.
Dole doka tayi aiki
Ologunagba ya ce PDP ba za ta zura idanu a karya dokokin kasa ba, don haka za su kai batun kotu.
Har ila yau, a jawabin na Ologunagba, ya nuna jam’iyyar hamayya ta PDP tayi imani cewa kotu za ta yi fatali da tsige Mahadi Gusau da aka yi daga kan mulki.
“PDP ta na duba abubuwan da suka faru a Zamfara, inda aka yi wa dokar kasa hawan-kaawara, kuma za ta dauki matakin da ya kamata.”
“A duk yadda ta kama, jam’iyyar PDP da mutanen jihar Zamfara ba za su bari kama-karya ta samu gindin zama ba, za a tashi tsaye, a je kotu.”
“Abin murna, jam’iyyarmu ta yarda kotu za su yi gaskiya, kamar yadda suka rika yi a baya domin kare kundin tsarin mulki da dokar kasa.”
Taron Gwamnonin APC
A makon nan aka ji cewa kowane Gwamnan APC zai hallara a garin Abuja inda za a sa labule domin tattauna batutuwan da suka shafi zaben shugabanni na kasa.
Akwai alamun cewa yadda aka yi kason kujerun majalisar NWC bai yi wa wasu gwamnonin jihohi da kusoshin jam’iyyar APC dadi ba, a dalilin haka ne za a zauna.
Asali: Legit.ng