Ba abin yarda ba ne: Kul PDP ta amince da Atiku a 2023 - Tsohon Mai magana da yawunsa
- Kassim Afegbua wanda ya taba zama mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar ya juya masa baya
- Wannan karo, Mista Afegbua ya fito yana nuna adawarsa a fili ga tsohon mai gidansa saboda siyasar 2023
- Tsohon Hadimin na Atiku Abubakar ya ce bai kamata PDP ta yi wani gigin tsaida shi takara a wani karon ba
Punch ta rahoto Kassim Afegbua yana kira ga jam’iyyar hamayya ta PDP cewa ka da ta yarda da shi, har ta kai ga ba shi tikiti a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Afegbua yana ganin bai dace jam’iyyar PDP ta maimaita kuskuren da ta yi a zaben 2019 ba, ta ba Atiku takara, ya bar Najeriya bayan ya sha kashi a hannun APC.
Maimakon ya yi koyi da shugaban Ukraine, tsohon hadimin ya zargi Atiku da tserewa Dubai bayan zaben 2019, ya bar su da barazanar gwamnatin nan mai-ci.
Atiku Abubakar ya shafe lokaci mai tsawo bayan zaben shugaban kasa a 2023, inda ya tare a Dubai, kasar UAE. Sai bayan watanni ne sannan ya dawo kasarsa.
Jaridar ta ce Afegbua ya bada wannan shawara a wani jawabi da ya fitar da hannunsa a ranar Lahadi, wanda ya yi wa take da ‘PDP 2023: Atiku Abubakar ya yi karya’.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsohon hadimin na Atiku ya na mai martani bayan jin shi yana cewa bai taba rasa tikitin PDP ba.
A cewar Afegbua, sau daya kurum Atiku ya taba tsayawa takara a karkashin jam’iyyar PDP tun kafuwarta. Shekaru kusan 24 da suka wuce aka kafa PDP a kasar nan.
A jawabin na sa, Afegbua ya ce kamata ya yi a ce tsohon mataimakin shugaban kasar yana kokarin hada-kan PDP, ba tunkaho da samun takarar shugaban kasa ba.
Atiku ya yi karya
"A 2019 ne kurum Alhaji Atiku Abubakar ya samu damar zama ‘dan takara a PDP a gangamin Fatakwal, inda ‘yan takarar Kudu suka yarda a bar ‘Yan Arewa kadai su nemi tikiti.”
“Saboda haka maganar cewa ‘Zan yi ta samun tikitin PDP’ ya saba tunani, hankali da zahiri.” - Afegbua
A maimakon ya dage sai ya yi takara a 2023, PM ta ce Afegbua ya yi kira ga Atiku Abubakar ya marawa wani matashin ‘dan takara daga Kudu domin ya karbi mulki.
Saura kwanaki 92 a gama lissafi
Kun ji cewa zuwa ranar 3 ga watan Yunin 2022 za a kammala duk wani zaben tsaida ‘dan takara da jam’iyyu za ayi a Najeriya na zaben shugaban kasa a 2023.
Kafin wannan lokaci, ‘yan takarar shugaban kasa irinsu Atiku Abubakar, da su karon kansu jam’iyyun siyasa da mutanen Najeriya za su san ina su ka dosa.
Asali: Legit.ng