Daruruwan mambobi a mahaifar dan takarar gwamna na PDP sun sauya sheka zuwa APC
- Yayin da zaben 18 ga watan Yuni na gwamnan jihar Ekiti ke kara matsowa, jam'iyyar APC ta yi sabbin mambobi a Efon Alaye
- Dandazon mambobin PDP a garin da dan takarar jam'iyyar ya fito, sun sauya sheka zuwa APC mai mulkin jihar
- Mutanen sun ce abubuwa sun dagule a PDP ba su da wani zabi da zarce shigowa APC dan ba da gudummuwarsu
Ekiti - Daruruwam mambobin PDP a garin Efon Alaaye, mahaifar ɗan takarar gwamna, Bisi Kolawole, sun sauya sheka zuwa APC.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta saka ranar 18 ga watan Yuni, 2022 a matsayin ranar zaɓen gwamnan Ekiti, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Dandazon masu sauya shekar sun bayyana cewa sun ɗauki matakin ne saboda ta kare wa PDP, komai ya rincaɓe, babu abin da ke tafiya dai-dai.
Sun kuma kara da cewa ba su yadda da jagorancin jam'iyyar PDP ba, kuma ba su da wani zabi da ya zarce su koma APC mai mulki.
Mutanen sun sanar da matakin komawa APC ne yayin ziyarar godiya da ɗan takarar gwamna karkashin APC, Biodun Oyebanji, ya kai musu.
Da yake jawabi a madadin sabbin mambobin, Ajayi Busuyi, ya tabbatar da goyon bayan su ga takarar Oyebanji, kuma ya jaddada cewa zasu yi aiki don APC ta samu nasara a zaɓen dake tafe.
Yace:
"Mun ɗauki matakin ficewa daga PDP ne saboda APC ta taka matakan samar da kyakkyawa kuma ingantaccen jagoranci ga al'ummar jihar Ekiti."
Kofar mu a bude take - APC
Chief Jide Awe, tsohon shugaban APC na jihar Ekiti, wanda ya karbi masu sauya shekan, ya yaba wa matakin da suka ɗauka, yace kofar APC a buɗe take ga duk mai son shigowa.
"Wannan abin jin daɗi ke sosai kuma muna maraba da yan uwan mu maza da mata zuwa tsagin kawo cigaba. A madadin jagorancin jam'iyya ina muku maraba kuma mun zama ɗaya."
Oyebanji, ya gode wa sabbin mambobin bisa matakin da suka ɗauka, ya musu alkawarin yin aiki tare domin matsar da jihar Ekiti zuwa mataki na gaba.
A wani labarin kuma mai kama da wannan Kwamishinan gwamnan APC ya fice daga jam'iyya, ya koma PDP
Kwamishinan harkokin waje na jihar Imo da APC ke mulki, Fabian Ihekweme, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya.
Fitaccen ɗan siyasan ya jagorancin dandazon masoya da magoya bayansa a APC zuwa sabuwar jam'iyyar da ya koma PDP.
Asali: Legit.ng