Janar Tukur Buratai ya yi magana game da sabon rade-radin zama Magajin Buhari a 2023

Janar Tukur Buratai ya yi magana game da sabon rade-radin zama Magajin Buhari a 2023

  • An fara yin kira ga Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai ya fito takarar shugaban kasa a Najeriya
  • Tsohon shugaban hafsun sojojin kasar ya tanka wannan jita-jitar, ya ce bai da sha’awar yin siyasa
  • Janar Tukur Yusuf Buratai ya fitar da jawabi na musamman ta bakin Janar Sani Usman Kukasheka

Tsohon shugaban hafsun sojoji na kasa, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya nesanta kansa daga neman takarar shugaban kasa a 2023.

Jakadan na Najeriya zuwa kasar Benin ya bayyana cewa bai fadawa kowa yana neman mulki ba. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi.

Hakan na zuwa ne bayan fastocin tsohon sojan sun fara yawo, ana jita-jitar zai yi takara a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa

A wani jawabi da ya fitar ta hannun tsohon mai magana da yawun bakin sojojin kasa, Birgediy Janar Sani Usman Kukasheka, ya karyata wannan rade-radi.

Jawabin da aka fitar

“Hankalin Jakadan Najeriya zuwa Jamhuriyyar Nijar, kuma tsohon shugaban hafsun sojojin kasa, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai ya zo ga kiraye-kiraye da fastoci da wasu ke yadawa, su na kiran shi ya shiga siyasa, ya nemi takarar shugaban kasa.”
Janar Tukur Buratai ya yi magana game da sabon rade-radin zama Magajin Buhari a 2023
Shugaban kasa tare da Tukur Yusuf Buratai Hoto: www.cfr.org
Asali: UGC

“Ya kamata a bayyana cewa Ambasadan (Tukur Yusuf Buratai) bai taba nuna sha’awar hakan ba.”
“Saboda haka wadannan fastoci da kiraye-kiraye ba daga wurinsa suka fito ba, kuma ba ya sha’awarsu.”
“Wasu mutane ne kurum su ke yin wannan aiki saboda dalilin da su kadai su ka sani.”

Godiya ga Buhari da masoya

“Janar Buratai yana kara jaddada kokarinsa da dagewarsa wajen yi wa kasa hidima a matsayinsa na Jakadan Najeriya zuwa kasar Jamhuriyyar Benin.”

Kara karanta wannan

IBB ga 'yan siyasa: Kar ku yi wasa da hadin kan 'yan Najeriya

“Yana godiya ga Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ba shi dama ya yi wa kasarsa aiki.”

Daily Trust ta ce a karshe ta bakin Janar Kukasheka (mai ritaya), Buratai ya godewa abokai da masu fatan alheri da suka nuna damuwarsu a game da lamarin.

Kwankwaso ya caccaki PDP da APC

A karshen makon da ya gabata ne ku ka ji labari cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya kyankyasa inda ya sa gaba a siyasa, inda ya yi wa PDP da kumaAPC kaca-kaca.

A wata hira da aka yi da Kwankwaso, ya soki salon tafiyar jam’iyyarsa ta PDP da APC, ya ce dukkaninsu ba su da abin da za su iya nunawa al'umma a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng