Kwankwaso ya kyankyasa inda ya sa gaba a siyasa, inda ya yi wa PDP da APC kudin-goro

Kwankwaso ya kyankyasa inda ya sa gaba a siyasa, inda ya yi wa PDP da APC kudin-goro

  • A wata hira da aka yi da Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki salon tafiyar jam’iyyarsa ta PDP da APC
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya na ganin babu abin da APC da PDP za su yo alfahari da shi a 2023
  • Tsohon Gwamnan na Kano ya fara yin kira ga jama’a su nemi wadanda za su kawo masu mafita

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi gwamna a jihar Kano sau biyu ya yi wa manyan jam’iyyun siyasar Najeriya watau PDP da APC kaca-kaca.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ‘dan siyasar ya ce jam’iyyun biyu duk ba su da abubuwan da za su nuna domin al’ummar kasar nan su zabe su a 2023.

Jagoran na Kwankwasiyya ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira da gidan rediyon Nasara FM. A yau 20 ga watan Fubrairu 2022 aka fito da hirar.

Kara karanta wannan

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa - Kungiyar Ibo

A cewar Rabiu Musa Kwankwaso, jam’iyyarsa ta PDP mai adawa da APC mai mulki, cike suke da ‘yan siyasan da bai dace mutane su sake kada masu kuri’a ba.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi kira ga al’ummar kasar nan su nemi jam’iyyar da za ta fitar da su daga cikin halin da wadannan jam’iyyu suka jefa kasar a ciki.

Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook

A nemi wata mafitar

“Ban ga abin da jam’iyyar PDP ko APC ba su nuna, ko su fadawa ‘Yan Najeriya domin su gamsu, su zabe su a zabe mai zuwa na 2023 ba.”
“Saboda haka ina tunani mutane su zauna, su yi tunanin jam’iyya da mutanen da ya dace su zaba domin ceto su daga halin da aka shiga.”

-Rabiu Kwankwaso

Tsautsayi a siyasar Kano

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Dalilin da ya sa Jonathan ya sha kashi a hannun Buhari da APC a zaben 2015

Tsohon ‘dan takarar shugaban kasar ya na ganin bai kamata ya dawo gida, ana gwagwarmayar siyasar Kano da shi ba, amma ya ce tsautsayi ne ya rutsa da shi.

An rahoto Kwankwaso yana cewa sun yi kuskuren damka mulkin Kano a hannun wadanda suka yi tunanin za su kawo gyara a zaben 2015, sai suka ga akasin haka.

Sanata Kwankwaso wanda ake ganin yana da burin takarar shugaban kasa a 2023 ya sake nuna inda ya sa gaba a wannan hirar a lokacin da ake tunnin zai bar PDP.

Rade-radi su na kara karfi cewa akwai mummunar baraka tsakanin tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano.

Abin da ya yi waje da Jonathan

Kwanakin baya kun samu labari cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin silar shan kasar Goodluck Jonathan da PDP ya na kan karagar mulki a zaben 2015

Sanata Kwankwaso ya ce tsohon shugaban kasar bai sa su wanene ya kamata ya tafi fa su ba, a haka Jonathan ya yi ta tara tarkace, ya dauka za su kai shi ga nasara.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Gwamna ya fadawa PDP gaskiya mai daci, ya ce mulki zai iya subuce mata

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng