Matashin dan takarar shugaban ƙasa a 2023 ya gana da IBB, ya nemi ya sa masa albarka
- Adamu Musa, ɗan shekara 40 a duniya dake neman gaje kujerar Buhari ya kai wa tsohon shugaban ƙasa ziyara a Minna, jihar Neja
- Matashin ya ce ya gana da Ibrahim Badamasi Babangida ne domin neman albarka, da kuma goyon bayansa a zaɓen 2023
- IBB ya yaba masa bisa nuna kwarin guiwa tare da jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su fito su karbi Najeriya
Minna, jihar Niger - Matashin ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar APC, Adamu Garba, a ranar Alhamis ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Ibrahim Badamasi Babangida.
Jaridar Channels tv ta rahoto cewa matashin ɗan shekara 40 a duniya ya gana da IBB ne a gidansa dake Minna, babban birnin jihar Neja.
Da yake jawabi ga manema labara jim kaɗan bayan ganawarsu, Garba ya ce ya ziyarci Minna ne domin neman sa albarka da kuma goyon bayan Babangida.
Sannan Kuma ya ƙara da cewa ya gana da tsohon shugaban mulkin soja ne domin sanar masa da kudirin shiga takarar kujera lamba ɗaya a shekara mai zuwa.
Wane kudiri matashin ke da shi?
Idan ya samu nasarar ɗarewa kujerar, Adamu Garba, ya yi alƙawarin ba da fifiko sosai wajen cigaban tattalin arziƙin ƙasa.
Ɗan takarar ya yi alƙawarin cewa zai kirkiri yankuna tara na tattalin arziki, zai yi wa ma'aikata garambawul domin yin aiki yadda ya kamata.
Ya kamata matasa su fito - IBB
Da yake jawabi, tsohon shugaban ƙasan ya yaba wa ƙarfin guiwar matashin tare da kiran matasa sun fito su karbi jagorancin ƙasa.
IBB yace matasan Najeriya na da ilimin da ake bukata, ƙarfi da kwakwalwar da zasu tafiyar da Najeriya kuma su magance kalubalen da suka addabi ƙasa.
Yayin da yake sa masa albarka IBB Ya ce:
"Abin da kake bukatar yi a yanzu shine ka fita ka tattara kan mutane masu tunani irin naka, masu shekaru irin naka, mafi yawan mu lokacin da muka shiga siyasa muna shekaru dai-dai da naku."
A wani labarin na daban kuma Gwamna Bello dake neman takarar shugaban ƙasa a 2023 ya nemi taimakon yan Najeriya kan cimma kudirinsa
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya roki shugabannin APC na jiharsa su fara nuna masa soyayya game da takara a 2023.
Bello, ɗaya daga cikin waɗan da suka ayyana takarar kujerar shugaban ƙasa, yace ya kamata gida su fara nuna masa tsantsar goyon baya.
Asali: Legit.ng