2023: Tsohon Gwamna ya fadawa PDP gaskiya mai daci, ya ce mulki zai iya subuce mata

2023: Tsohon Gwamna ya fadawa PDP gaskiya mai daci, ya ce mulki zai iya subuce mata

  • Sule Lamido ya na ganin cewa ba dole ba ne mulki ya bar APC ya koma hannun jam’iyyar PDP a 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya ce dole sai an samu hadin-kai kafin PDP ta iya kafa gwamnati
  • Alhaji Lamido ya kai wa shugabannin PDP ziyara a Abuja, inda ya yi kaca-kaca da gwamnatin APC

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ja-kunnen jam’iyyarsa ta PDP da cewa idan har ta yi sake, zata cigaba da zama ‘yar adawa ko a 2023.

Vanguard ta rahoto Alhaji Sule Lamido yana cewa muddin jam’iyyar PDP ta gagara shawo kan batun inda za a kai shugabanci, APC na iya cigaba da mulki.

Ganin yadda ake ta surutu kussan kullum a kan inda za a kai tikitin PDP, Sule ya ce sai jam’iyya ta na nan daram sannan za a fara maganar wa za a ba takara.

Kara karanta wannan

ASUU: Ba dole sai an shafe wata ba, a kwana 7 za mu dawo aiki idan Gwamnati ta ga dama

Tsohon gwamnan ya na ganin idan PDP ta sha kashi a zaben 2023, Najeriya ta tashi daga aiki kenan. A na sa ra'ayin jam'iyyarsa kadai za ta iya rike kasar.

“Idan mu ka gaza samun mulki a zaben 2023, watakila karshen Najeriya ta zo kenan.” - Sule Lamido.

PDP - NWC sun yi baki

Jigon na PDP ya bayyana wannan ne a wajen wani zama da ya yi da ‘yan majalisar NWC da tsofaffin gwamnonn PDP a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Sule ya yi kira ga gwamnonin PDP da ke kan mulki a yau su yi aiki da tsofaffin gwamnonin kasar domin a karfafa jam’iyyar hamayyar a zabe mai zuwa na 2023.

Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar PDP ta na kamfe Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jam'iyya kafin 'Dan takara

“Idan ba mu yi abin da ya dace ba, Najeriya ta na cikin matsala. Sai da jam’iyya ake kafa gwamnati. Jam’iyyar da ba ta da kan gado, ba za ta kawo gwamnati ba.”

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

“Shiyasa ku ke ganin jam’iyyar APC mai mulki ba ta da kan gado.”
“Duk jam’iyyar da ta ke a wargaje, babu tsari ba za ta haifar da ‘da mai ido ba. Ku duba abin da ke faruwa da Najeriya yanzu da (gwamnatin) APC.”

– Sule Lamido.

2023 sai an shirya

“Za a sha wahala a gwagwarmayar zaben 2023, za a bukaci kokari, hakuri da tsayin dakanmu a siyasa, amma na san mu na da abin da ake bukata.”

Tribune ta ce shugaban jam’iyyar adawar, Dr Iyorchia Ayu, ya ji dadin yadda tsofaffin gwamnonin suka kawo masa ziyara, ya ce jama’a sun shirya zaben PDP.

Emefiele a APC?

Ku na da labari cewa duk da babu ruwansa da siyasa, wasu masu rike da madafan iko sun hurowa Godwin Emefiele wuta ya fito takarar shugaban kasa a 2023.

Kira-kiraye ga Gwamnan CBN ya fito takarar shugaban kasa ya fara karfi, saboda ana kyautata zaton ya samu fada a wajen shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

Kotu ta sharewa Kwankwasiyya hanyar takarar Shugaban PDP a Arewa a sa’ar karshe

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng