Gwamnoni, Sanatoci, tsofaffin masu mulki 100 sun hadu domin ceto Najeriya kafin zaben baɗi

Gwamnoni, Sanatoci, tsofaffin masu mulki 100 sun hadu domin ceto Najeriya kafin zaben baɗi

  • Wasu da suka kira kansu da ‘The 2022 Committee’ sun yi kwanaki uku a jere su na taro a Legas
  • Makasudin zaman na su shi ne ganin yadda za a shawo kan matsalolin kasar nan kafin zaben 2023
  • Nduka Obaigbena da Kashim Ibrahim-Imam sun fitar da jawabi bayan sun kammala taron na su

Lagos - Manyan mutane kimanin 100 da su ka kunshi ‘yan siyasa, masana da kwararru sun yi wani taro a Legas domin fito da yadda za a ceci Najeriya.

Jaridar This Day ta ce taron ya hada da gwamnoni 14 masu-ci da tsofaffin gwamnonin jihohi 13 da wasu shugabannin majalisar dattawa uku da aka taba yi.

Wadannan jagorori a karkashin inuwar ‘The 2022 Committee’ sun ce ya zama dole a samar da zaman lafiya a kasa kafin a fara yin maganar takara a 2023.

Kara karanta wannan

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

‘Yan kwamitin na ‘The 2022 Committee’ sun fitar da jawabin bayan taro ne ta bakin shugabanninsu; Nduka Obaigbena da Kashim Ibrahim-Imam.

Obaigbena da Ibrahim-Imam sun yi magana

Obaigbena da Ibrahim-Imam sun bayyana cewa kwamitin na su ya yi aiki a kan tattalin arziki, tsaro da shirin mika mulki domin ganin halin da ake ciki a yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The 2022 Committee
'Yan The 2022 Committee Hoto: thenigeriadaily.com, dsr
Asali: UGC

Kwamitin ya yi kira ga duk masu kishin-kasa da suke sha’awar a kawo gyara a Najeriya, su shigo cikinsu domin ganin an samu kasar da za ayi alfahari da ita.

Kujerar siyasa su ke nema?

A cikin wadannan mutane 100, babu wanda ba zai iya rike shugabanci na matakin kasa ba. Asali ma akwai masu harin kujerar shugaban kasa a 2023 a zaman.

Amma duk da haka, a wani rahoto da ya fito daga The Cable, kwamitin ya sanar da jama’a cewa bai da nufin yi wa wani ‘dan takara ko jam’iyyar siyasa aiki.

Kara karanta wannan

Jerin matsaloli 6 da Kwankwaso yake bukatar ya tsallake kafin ya shiga Aso Rock a 2023

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa jawabin da aka fitar bai kunshi sunayen wadanda aka yi zaman da su ba, amma an yi taron ne daga ranar Juma’a zuwa Lahadi.

Punch ta ce daga cikin wadanda aka iya gani a wajen zaman akwai Anyim Pius Anyim, Bukola Saraki, Gbenga Daniel, Ikedi Ohakim da Sanata Iyiola Omisore.

Masu gudu su gudu

A ranar Talata ne aka ji CJN ya maidawa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami martani kan zargin kotu da yake yi da kawo cikas a binciken marasa gaskiya.

Tanko Muhammad ya ce ba daidai ba ne Minista ya daura laifi ga Alkalai bayan gwamnati ce ta ke dauko shari’ar da sun fi karfinta, sai ta gagara kare kanta a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng