2023: Dalilai 2 da suka sa Farfesa Osinbajo ba zai yi takara da Bola Tinubu ba - Jigon APC
- Daniel Bwala ya ce muddin Asiwaju Bola Tinubu yana neman takara, ba za a ga Yemi Osinbajo ba
- Ra’ayin Bwala shi ne mataimakin shugaban kasar ba zai iya kalubalantar tsohon mai gidansa ba
- Ko da Tinubu zai nemi shugabanci, shi Farfesa Osinbajo bai fito ya fadi matsayar da ya dauka ba
Abuja - Daya daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki, Daniel Bwala, ya yi ikirarin Farfesa Yemi Osinbajo ba zai yi takara da Asiwaju Bola Tinubu ba.
Daniel Bwala ya bayyana wannan ne a lokacin da aka gayyace shi ya yi magana a gidan talabijin nan na Channels TV a ranar Talata, 8 ga watan Fubrairu 2022.
Bwala ya fito karara yana cewa mataimakin shugaban kasar ba zai ja da tsohon mai gidansa da yake fashin baki a cikin shirin siyasa na Politics Today a jiya.
A cewar Daniel Bwala, Osinbajo bai da sha’awar neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023. Ita ma jaridar Punch ta kawo wannan rahoto a safiyar ranar Laraba.
Jagoran na jam’iyyar APC ya ce Mai girma Osinbajo ya fahimci rayuwa, ya san irin taimakon da tsohon mai gidansa ya yi masa a siyasa, don haka zai yi halacci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ina tunani na san hikimar mataimakin shugaban kasa Osinbajo na kin fitowa takara, kuma yana kokarin toshe duk wani yunkurin hakan.”
“Ya fahimci a rayuwa duk wanda ya yi maka alheri, akwai bukatar ka yi masa sakayya. Uban gidansa ya mara masa baya na shekaru takwas.”
“Saboda Asiwaju (Bola Tinubu) ya nuna sha’awar takara, hankali ma zai fada maka (ba a doka ba) cewa ba daidai ba ne Osinbajo ya fito takara.”
“Na biyu kuma shi ne wasu su na ganin idan wanda ya taimake ka yana neman wani abu, to abin da ya kamata da kai shi ne ka mara masa baya.”
Masoyan Osinbajo su goyi bayan Tinubu
“Idan bai yi nasara ba, zai dawo ya goyi bayanka, ba za ka kalubalance shi ba. Tun da Osinbajo ba zai yi takara ba, sai ya fadawa mabiyansa su bi bayan Tinubu.”
“Idan ya cigaba da kyale mutane su na tafiya a cikin duhu, za a samu rudani tsakanin magoya bayansa (Osinbajo) da kuma magoya bayan Tinubu.” – Bwala.
Takarar Kwankwaso a 2023
A baya kun samu rahoto cewa Rabiu Musa Kwankwaso wanda yake da tarin magoya-baya, da alamun cewa ya na da burin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Kafin Sanata Kwankwaso ya kai ga cin ma burinsa yana bukatar karbuwa wajen ‘yan siyasan kudu da kuma kafuwa a jam’iyya, sannan yana bukatar ya tanadi kudi.
Asali: Legit.ng