Gwamnan PDP ya dubi Atiku ido da ido, ya fada masa wanda za su marawa baya a 2023
- Masu neman takarar shugaban kasa a Najeriya a zabe mai zuwa na 2023 su na cigaba da fafutuka
- Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom ya sha alwashin cewa za su goyi bayan wanda zai tsare al’umma
- Ortom ya bayyana wannan ne a lokacin da ya hadu da tawagar Atiku Abubakar a garin Makurdi
Makurdi – Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya yi zama da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar a garin Makurdi.
Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci jihar Benuwai domin ya taimakawa ‘yan gudun hijira. Amma ana ganin ziyarar ta na tattare da neman irin siyasa.
A wajen wannan haduwa, AIT ta rahoto Mai girma Samuel Ortom yana mai bayani a game da ‘dan takarar da mutanen Benuwai za su zaba a 2023.
Samuel Ortom ya bayyana cewa jihar Benuwai ba za ta goyi bayan wani ‘dan takarar shugaban kasa ba sai wanda zai tabbatar da kare ran al’umma.
“Mutane da gwamnatin jihar nan (Benuwai) su na bukatar wanda zai iya kare ransu da dukiyoyinsu, baya ga wasu abubuwan.” – Samuel Ortom.
Kamar yadda mu ka samu rahoto daga gidan talabijin, Wazirin na Adamawa da ‘yan tawagarsa sun zauna da Ortom ne a ranar 6 ga watan Fubrairu 2022.
Tawagar tsohon mataimakin shugaban kasar da ta je gidan gwamnatin na jihar Benuwai ta hada da shugaban kwamitin tsare-tsarensa, Raymond Dokpesi.
Har dai ya bar garin Makurdi, The Cable ta ce Atiku Abubakar bai bayyana cewa yana da niyyar tsayawa takarar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa ba.
Za mu ci zabe - Ortom
Sai dai Gwamnan ya nuna cewa ko me zai faru, yana sa ran jam’iyyar PDP za tayi nasara a 2023.
A gefe guda, Ortom ya caccaki gwamnatin tarayya da Muhammadu Buhari yake jagoranta da kin daukar matakin da ya dace domin kare mutanen Benuwai.
An yi fushi da Atiku
A baya an ji Gwamnan Benuwan ya ce har mutanensa sun fara fushi da yadda Atiku Abubakar ya yi watsi da su, sai ga shi ya yi kyautar da ta wanke laifinsa.
Atiku yana rike da babbar sarauta a kasar Tiv, amma kafin yanzu bai ba mutanen Benuwai gudumuwa ba a lokacin da 'yan bindiga suka addabe jihar.
Asali: Legit.ng