Lissafin Tinubu zai canza, Osinbajo yana daf da tsayawa takarar shugaban kasa

Lissafin Tinubu zai canza, Osinbajo yana daf da tsayawa takarar shugaban kasa

  • Ana ba mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo shawara ya tsaya takara a jam’iyyar APC
  • Akwai yiwuwar Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana nufinsa na neman shugabanci a zaben 2023
  • Na-kusa da mataimakin na Buhari sun ce maganar za ta fito fili ne bayan zaben shugabannin APC

Abuja - Mai girma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kammala shirye-shiryen sanar da niyyarsa na neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Wani rade-radi da yake yawo daga jaridar This Day ya bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo zai fito takara ne bayan APC ta yi zaben shugabannin na kasa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutanen Osinbajo sun kyankyasa wannan a karshen makon da ya gabata, suka nuna mai gidansu zai jarraba sa’ar ta sa.

Rahoton ya shaida mana cewa Farfesa Osinbajo ya samu goyon-bayan babban mai gidansa a gidan cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye kan neman wannan kujera.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a Twitter: Dan Elrufa'i ya yiwa dan takara a 2023 ba'a

Ka rubuta ka ajiye

“Ka rubuta, ka ajiye, Osinbajo zai yi takara, kuma zai bayyana nufinsa bayan an kammala zaben shugabannin jam’iyyar na kasa.”
“An shirya tsaf, har an kammala tuntubar duk da za ayi. Da alamun za a samu nasara, goyon baya da ake samu sun karfafa Osinbajo.”
Fadar shugaban kasa
Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Majiyar ta ce cikin masu marawa Yemi Osinbajo ya nemi takara a APC har da matasan kasar nan. Don haka zai yi watsi da zargin yana neman cin amanar Bola Tinubu.

“Daga Arewa zuwa Kudu, ina ne ya ziyarta inda ba a ji ana neman ya fito takara ba? Ya cancanta, kuma ya dace, sannan ya san matsalolin kasar.”
“Kuma mafi muhimmancin abu shi ne ya san yadda zai tallata kan shi – To me zai hana shi takara? Me zai sa hassadar wasu ta tsaida shi?” - Majiyar.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Burin Tinubu, Osinbajo da Fayemi ya raba kan Gwamnonin Yarbawa a APC

Jaridar ta ce ko da Osinbajo bai bayyana matsayarsa ba, ya na ta zama da wasu manyan mutane wadanda suke ba shi shawarar ya nemi kujerar shugaban kasa.

An gamsu da Osinbajo?

An fara zuga Osinbajo ya tsaya takara ne tun bayan da ya rike Najeriya na rikon kwarya a lokacin da Buhari yake jinya, kuma aka gamsu da irin gudun ruwansa.

A lokacin ne aka tsige Lawal Daura daga mukamin sa na shugaban hukumar DSS bayan ya aika wasu jami’an DSS su zagaye gidan shugabannin majalisar tarayya.

Ko bayan dawowar Buhari daga Birtaniya a 2017, ya bar mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya cigaba da rikon kwarya, har sai ya gama murmurewa a Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng