Yadda Shugaban kasa na rikon-kwarya Osinbajo ya sa aka kama Shugaban DSS Lawal Daura
Jaridar Premium Times ta bada rahoto tiryan-tiryan na yadda aka yi ram da Shugaban Hukumar tsaro na DSS jiya a fadar Shugaban kasa. Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bada wannan umarni a jiya Talata.
An tsige Lawal Daura daga mukamin sa ne bayan ya aika Jami’an sa sun zagaye harabar Majalisar Tarayya. Mai ba Shugaban kasa shawara game da sha’anin tsaro watau Babagana Monguno ne ya bayyanawa Osinbajo abin da ya faru.
Nan take Shugaban kasar na rikon kwarya ya kira wani taro cikin gaggawa na manyan Jami’an tsaron kasar. Ko da Mukaddashin Shugaban kasa ya tambayi dalilin da ya sa yayi wannan danyen aiki, amsar da Shugaban DSS din ya bada ta ba sa mamaki.
Lawal Daura ya fadawa Yemi Osinbajo cewa Shugaba Buhari ne ya nada shi wannan aiki kuma shi kadai ne ya isa ya tambaye sa dalilin da ya sa yayi wani abu. Daga jin haka, nan take Osinbajo ya sanar da cewa ya tsige Lawal Daura daga matsayin sa.
KU KARANTA:
Bayan nan ne Yemi Osinbajo ya fadawa NSA Munguno cewa ya mika Daura hannun jami’an SARS domin a bincike sa. Daga nan ne Dogarin Osinbajo ya sa aka garkame Daura sannan aka nemi motar Shugaban DSS din ta bar fadar Aso Villa.
Kamar yadda mu ka samu labari, kafin nan dama Mataimakin Shugaban kasar yayi magana da Shugaba Buhari inda ya fada masa cewa Lawal Daura yana aiki da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki. Daura dai bai san duk an yi wannan ba.
Wannan abu dai duk ya faru ne kamar mafarki. Kawo yanzu Mukaddashin Shugaban Kasa Osinbajo ya nada Matthew Seiyefa a matsayin wanda zai rike ofishin Shugaban DSS kafin ayi nadin din-din-din bayan sallamar Lawal Daura daga aiki da aka yi
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng