Rikicin Shekarau v Ganduje ya hana APC ta iya nada Shugaban Jam’iyya a jihar Kano

Rikicin Shekarau v Ganduje ya hana APC ta iya nada Shugaban Jam’iyya a jihar Kano

  • Kwamitin rikon kwarya da shirya zabe na shugabannin APC ya rantsar da shugabanni daga jihohi
  • An rantsar da shugabannin duka jihohin kasar nan dazu ban da na Kano da Sokoto a birnin Abuja
  • Har yanzu da aka tabbatar da shugabannin jihohi, ba a dinke barakar Ganduje da su Shekarau ba

Abuja – A jiya ranar Alhamis, 3 ga watan Fubrairu 2022 ne kwamitin rikon kwarya na APC ya rantsar da shugabannin jam’iyya na rassan jihohi a Najeriya.

Rahoton da mu ka samu daga jaridar Punch ya bayyana cewa an rantsar da shugabannin ne a sakariyar jam’iyyar APC mai mulki a birnin tarayya Abuja.

Babban labarin da aka samu shi ne Ahmadu Haruna Danzago da Abdullahi Abbas ba su cikin wadanda aka rantsar tare da ragowar shugabanni daga jihohi.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin rage haihuwa a Nigeria

A jam’iyyar APC na reshen jihar Kano, ana ta rigimar shugabanci tsakanin Ahmadu Haruna Danzago da Abdullahi Abbas wanda ya dade a kan mukamin.

Bangaren Sanata Ibrahim Shekarau su na tare da Danzago wanda ya taba yin shugaban CPC a Kano. A gefe guda, gwamnatin Ganduje na goyon bayan Abbas.

Da aka tashi rantsar da shugabannin jihohi a jiya, ba a gayyaci duka bangarorin na jihar Kano ba. Har yanzu ana kokarin yin sulhu ne ga kuma zabe na kasa ya zo.

Ganduje a Kano
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje Hoto: @ahmed.princegandujiyya.9
Source: Facebook

Sakataren APC na rikon kwarya na kasa John Akpanudoedehe ya wakilci Mai Mala Buni wajen rantsar da shugabannin da aka zaba tun karshen shekarar bara.

Martanin jagoran G7

Malam Ibrahim Shekarau ya zanta da ‘yan jarida bayan rantsuwar da aka yi a Abuja, ya ce za su 'dan saurara su ga ko uwar jam’iyya za ta sabawa umarnin kotu.

Tsohon gwamnan kuma Sanatan na Kano ta tsakiya mai-ci ya ce kotu ta tabbatar da tsagin Danzago a matsayin sahihin shugaban jam’iyya na reshen jihar.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan da suka yi nasara da wadanda suka sha kasa yayin da APC ta nada shugabanni

Jaridar ta nemi tuntubar bangaren Mai girma gwamna Abdullahi Ganduje, amma hakan ya faskara.

Rikicin Sokoto

Haka lamarin yake a game da reshen APC na jihar Sokoto inda tsohon gwamna, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Abubakar Gada suke ta rikici.

Uwar jam'iyya ba ta gayyaci Alhaji Isa Achida da Mainasara Abubakar wajen bikin rantsuwar ba.

Yadda ta kaya a APC

Dazu kun ji cewa wasu daga cikin kusoshin APC mai mulki da suka rasa ikon jam’iyya a hannun gwamnonin jihohinsu sun hada da wasu Ministoci da Sanatoci.

Adamu Adamu, Ovie Omo-Agege, Gboyega Oyetola sun yi galaba a kan abokan fadansu. Su Festus Keyamo, Yusuf Tuggar, da Rauf Aregbesola duk sun tashi a babu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng